VIDEO:”Akwai gashin ANNABI SAW a wajena ina jiƙawa mutane su sha don samun falala”—Ƙaribulla

A wani hoton bidiyo shahararren malamin addinin Islama kuma jagoran ɗariƙar ƙadiriyya Sheikh ƙaribulla Sheikh Nasiru Kabbara ya bayyana cewa akwai gashin fiyayyen halitta MANZON TSIRA ANNABI MUHAMMADU SAW a wajensa kuma yana jiƙa shi a ruwa ya bawa jama’a su sha domin samun tabarraki.

Ga bidiyon nan daga ƙasa.

Masu Alaƙa:

Abubuwan da suka halaka Malam Abduljabbar

Ra’ayin: Yasir Ramadan Gwale

Son shuhura da neman suna da mugun girman kai sune abinda suka halaka Abdul-Jabbar Kabara. Bayan gaskiya ta bayyana a gare shi cewar abinda yake kai ba daidai bane kuskure ne, maimakon ya karbi gaskiya, amma girman kai da kokarin burge gamagarin mabiyansa ya hana shi karbar gaskiya, yau gashi hakan ya kaishi ya baro.

Sau da yawa daman haka mutane masu neman suna da sun gurgewa suke karewa. Girman kai ya rufe musu ido su ki karbar gaskiya bayan ta bayyana a gare su cewar abinda suke kai kuma suke kira kuskure ne ko bata ne ba daidai bane, amma su rufe idonsu su makancewa gaskiya.

Mutum a wayi gari yace ya san wani ilimi da babu wanda ya sani sai shi. Ko kuma yace duk duniya ba wanda ya gano wani abu na ilimi sai shi. Kaga tun nan jahilci ya bayyana, duk garin neman suna da son burge gamagarin mabiya wanda banda ihu da hayaniya ba abinda suke taimakonsa da shi.

Mu kiyayi son shuhura da son lallai sai mun burge mutanan da babu wani abu da zasu amfanemu da shi illa su kaimu su baro. Allah ka nuna mana gaskiya ka bamu ikon binta, ka nuna mana karya ka bamu ikon guje mata. Amin.

Yasir Ramadan Gwale
16-12-2022

Views: 5

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *