Ɗan’uwan Abduljabbar uwa ɗaya uba ɗaya ya bayyana hukuncin masu zagin ANNABI SAW

LABARIN MAL.ABDULJABBAR .

Labarin mal. Abduljabbar labari ne na masu wuce gona da iri a cikin adawa .

Labarin Abduljabbar labari ne na rikicin Izala da Darika a Kano da kasa baki daya . Daga karshe azarbabiyar Abduljabbar ta jefashi rame .

Abduljabbar dan Darikar Qadiriyyah ne wadda hedikwatarta a Kano ne , kamar yadda Kano tana cikin hedikwatocin Darikar Tijjaniyyah . Haka kuma daga baya Kano ta zama daya daga cikin hedikwatocin bangarorin Izala , musamman bangaren Salafiyyah , a kasar nan .

Abduljabbar ya taso ne a cikin zafin rikicin martanoni tsakanin malaman Darika da takwarorinsu na Izala da Salafiyyah . A lokacin da ya ga shima kamar karfinsa na ilimi ya kawo sai ya shiga cikin irin wannan rikici na mayar da martanoni .

Babban abinda ko yaushe bangarorin Izala wadanda suka kebancewa kansu sunan “Ahlussunnah” suke godogo da shi shine kafa hujjah daga Kitabu da Sunnah da fassarar Salaf . Amma sun fi mayar da hankali sosai akan karatun hadisi , da tabbatar da ingancin hadisai ko rauni . Shi ma Abduljabbar sai ya shiga cikin wannan husuma ta ilimin hadisi , domin ya tabbatar wa abokan jayayyarsa cewa shima fa ba a barshi baya ba a cikin wannan fanni .

A daidai wannan lokaci kuma sai Kano ta zama daya daga cikin hedikwatocin Shi’a na kasa (Kano ko da me ka zo an fika) . Malaman Darika a Kano sun rabu gida biyu game da hulda da Shi’ah – yayin da mafi yawansu suke dari-dari da ita akwai wadanda suka sakar masu jiki . Abduljabbar yana cikin wadanda suka tasirantu da ra’ayoyin Shi’ah , musamman matsayinsu game da Ahlul Baiti . Sai ya fara karanta littafansu , wadanda suke dauke da suka ga Sahabbai , da rashin amincewa ga Hadisan da aka ruwaito kai tsaye daga Annabi (saw) . Da kuma ya tafi Iraq domin karo karatu sai ya kara haduwa da ‘yan shi’ah , da tasirantuwa da akidunsu da mawakif nasu akan Sahabbai da Hadisai .

Daga nan ne Abduljabbar ya yi shawarar ya fito da sabuwar hanyar yakar ‘yan Izala wadda a kasar nan babu wanda ya taba gwadata – ita ce hanyar rusa Sunnah kwata-kwata – wadda ita ce ‘yan Izala suke tinkaho da ita . Kafin hakan babu wani malami da ya taba gwada wannan , saboda dukkan ‘yan Darika sun yarda su Ahlussunnah ne , ba su da rikici da Sunnar Manzon Allah (saw) . Rikicinsu da fassarorin ‘yan Izala ne . Suma ‘yan Izala , malamai daga cikinsu , suna cewa e! ‘yan Darika Ahlussunnah ne , amma a faffadar ma’anar kalmar , su kuwa su ne kebantaccin Ahlussunnah .

Wani tasiri kuma da shi’ah , musamman ta bangaren Zakzakiyyah ta yiwa Abduljabbar shine fitowa fili “gaba-gadi” a tunkari abokan rikici . Ya kasa fahimtar cewa su Zakzakiyyah da gwamnati ne suke “gaba-gadi” , amma a abinda ya shafi akidun shi’ah , musamman abunda ya shafi Sahabbai , takiyyah su ke yi . Abduljabbar bai koyi hikimar “Takiyyah” ba , saboda ya dauki cewa idan dai bai cire rigarsa ta Ahlussunnah ba zai iya fadar komai da sunan “tattaunawar ilimi” .

Abduljabbar ya fara ne da kokarin tabbatar da cewa mafi yawan ibadodin da ‘yan Izala suka yarda da su ba bisa Sunnah su ke ba , bisa bidi’o’in da Sahabbai suka kirkiro aka ginasu . Don haka sai ya fara bayanai a kan “bidi’o’in Sahabbai” . A nan sai ya yi tarkizi a kan Sayyiduna Umar , abinda ke kara nuna tasirin shi’ah a kansa . Ya yi ta bayanai game da “bidi’o’i hamsin da Umar ya shigo wa musulunci da su” .

Babban abinda Abduljabbar ya kasa ganewa a lokacin da ya fara wannan aiki gaba-gadi , shine cewa yana soke dukkan fikihun da dukkan musulmin da ba su yin shi’ah suke addini da shi , ba sai ‘yan Izala kawai ba . Bai gane ya sa kafar wando daya da dukkan musulmi ba .
Yana fara wannan malaman gidansu suka fahimci hatsarin da zai jawo masu idan aka yiwa gidansu kudin goro a kan akidunsa , sai suka nemi taka mashi burki . Wannan ya haddasa sabani tsakaninshi da ‘yan uwanshi , har ya raba gari da su , ya assasa kungiyarsa da da’awarsa .

Bayyanar Google ta ba Abduljabbar dama ya leka wasu rubuce-rubuce na mulhidai da zindikai daga cikin musulmi , da kuma mustashrikun daga cikin malaman kiristoci , wadanda suke aibata Manzon Allah (saw) da Sahabbansa , suke yiwa hadisai mummunar fassara domin su yi zagi ga janibin Annabi (saw) . Wannan kuwa sai ya kara karfafa Abduljabbar a kan ra’ayinsa na rusa Sunnah .

Nan take sai Abduljabbar ya fara kutsa kai a cikin wannan manhaji na soke hadisai . Babbar manufarsa ita ce rusa ingancin Sahihu Bukhari da Sahihu Muslim , sai sauran littafan hadisi su biyo baya . Usulubinsa shine ya tabbatar da cewa Sahabbai ne da kansu suka kirkirawa Annabi (saw) karya domin su rusa Addininsa bayansa . Wannan kuma kocokaf usulubin shi’ah ne . Sauran maruwaita kuwa Abduljabbar ya ce dukkansu sun san karairayi ne Sahabbai suka kirkirawa Annabi(saw) , amma suka ci gaba da boye hakan tsawon shekaru fiye da dubu ! Wannan kai tsaye shine matsayin shi’ah game da hadisan Sunnah .

Me zai tabbatar cewar Sahabbai adawa suke yi da Annabi (saw) , suna kokarin rusa mashi Addini ? Shine sai Abduljabbar ya dingi dauko maganganun malaman shi’ah da na zindikai da mulhidai , da na malaman kiristoci (dukkan abubuwan da Abduljabbar ya fadi karantosu ya yi a wasu wurare ba shine ya ganosu ba , kamar yadda ya ke riyawa) , wadanda suke nuna cewa wai Sahabbai sun ci mutuncin Annabi (saw) , ko kuma sun shigo da wani abu cikin shari’ah wanda ba zai yiwu a ce daga Annabi (saw) ne ba (wannan shine malamai suke kira da sukar hadisi ta ilimin “Dirayah” , wato ilimin fahimtar ko abinda hadisi ya ke karantarwa ya yi daidai da shari’ah ko bai yi ba , a maimakon sukar hadisi da ilimin “riwayah” , wato la’akari da ingancin isnadi .Abduljabbar duka biyu din ya ke amfani da su , sai dai ya saba wa malamai da suka ce ba a sukar hadisi da Sahabin da ya ruwaitoshi , saboda Sahabbai dukkansu adilai ne . Sai ya dauki maukifin ‘yan shi’ah cewar illar hadisi ita ce Sahabi , babu la’akari da wadanda suka biyo bayansa a isnadi) .

Musulmi a kasar nan suna karanta wadannan hadisai da sharhohinsu tun daga ranar da musulunci ya shigo kasar nan , amma ba su taba jin wadannan fassarori ba na Abduljabbar . Amma sai gashi yana kawosu – kamar yadda Alkalin da ya yi shari’ah ya ce – “ba tare da nuna kalmomin a zahiri ba a cikin hadisan , ba kuma fassara ya yi da ma’ana ba , sai dai wai – kamar yadda Abduljabbar din ya fada – ya yi fassara ne bisa ‘shubhul ma’ana’ ” . Don haka a wurin dukkan musulmin kasar nan , in banda ‘yan shi’ah , tunda dai wadanda Abduljabbar ya ce su suka aibata Annabi (saw) , ba ta tabbata su suka yi ba , to shi Abduljabbar din dai daga bakinsa aka ji , don haka shine ya ke aibata Annabi (saw) da kansa . Wannan ya jawo dukkan bangarorin musulmin Kano , wadanda suke karba sunan “Ahlussunnah” , ko da kuwa da “faffadar ma’anar” kalmar , suka yi maja domin yakar wannan fasadi da ya bayyana , wanda shi’ah ne kawai a rigar sunnah .

Malaman “Maja” sun yi nasara a kan tilastawa gwamnatin Kano ta labta Abduljabbar kotu . Alkali kuwa ya yi masa hukunci da matsayi malaman malikiyya . Kamar yadda Alkalin ya tabbatar , a cikin littafin “As-shifa’ ” wanda ko yaushe ake karatu a gidan su Abduljabbar , an fadi cewa matsayar Imamu Malik ita ce : wanda duk ya fadi wata aibatawa a kan Annabi (saw) , sai ya ce wani ne ya ce , sai ta tabbata wani din bai ce ba , to shi din ne ya fada kenan , kuma hukuncinsa kisa ne .

A lokacin da Abduljabbar ya fito gaba-gadi domin yada akidun shi’ah a cikin rigar Sunnah , don kawai ya samu nasara a kan ‘yan Izala , ya gafala da wannan karatu na ciki “As-shifa’ ” . Gashi yau karatun ya ci shi . Haka kuma ya gafala cewa zai saka kafar wando daya da dukkan bangarorin musulmi da ba ‘yan shi’ah ba . Gashi yau “Maja” ta ci shi . Sannan ya gafala da cewar duk da ana cewa kasar nan kowa yana da ‘yancin fadin abinda ya ga dama amma a Kano ana taba yin shari’ar musulunci . Gashi yau shari’ar musulunci ta ci shi .

Jama’ah a daina azarbabiya a cikin adawa .

Views: 8

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *