Shekarar 2022 dai ta ƙare yanzu haka yau mun shigo sabuwar shekara ta 2023 yayin da wasu ke murnan burinsu ya cika wasu kuma cewa suke sun ma fitar da ran cikar burin nasu a daren jiya da shekarar ke ƙarewa.
Wata matashiya mai amfani da shafin Facebook tayi comments a rahoton BBc Hausa da suka tambayi mabiyansu ko burinsu ya cika a shekarar 2022 sai tafe ita dai ta fitar da ran yin aure a shekarar ga rubutunta nan daga ƙasa.

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Dauda Biu a matsayin shugaban Hukumar FRSC na ƙasa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da nadin mataimakin shugaban rundunar corps, Dauda Ali Biu, a matsayin babban jami’in hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC).
An nada Dauda Biu a matsayin shugaban hukumar corps a watan Yulin 2022 lokacin da Boboye Oyeyemi ya yi ritaya daga aikin.
Kakakin hukumar FRSC, Bisi Kazeem, ya ce kwararren ma’akacin hanya ya fito ne daga karamar hukumar Hawul ta jihar Borno kuma haifaffen garin Zaria ne a jihar Kaduna.
Ya shiga aikin hukumar FRSC ne a shekarar 1988 kuma ya samu hazaka da kwazo da sadaukar da kai ga mukamin mataimakin marshal kuma ya rike mukamai da dama.
Marshal din yana da digiri na biyu a fannin kasuwanci (MBA) da kuma digiri na farko a fannin lissafi a jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya.
Views: 34
