Abubuwa ukku da dattawa ke amfani da su wajen kasa samari a gun ƴan mata

Wani bincike ya nuna cewa dalilai biyu zuwa ukku ne ke sawa dattawan wannan zamani ke kasa samari masu jini a jika a wajen ƴan mata inda ake nuno hotunan dattawan na zaɓar zuƙa-zuƙan ƴan mata sa’anni jikokinsa suna aure su ga dalilan kamar haka.

Na farko dai wasu ƴan matan suna da ra’ayin cewa dattawa sun fi kula da macce tare da riƙe ta da kyau saboda sun san muhimmancinta fiye da samari waɗanda abunda bai taka kara ya karya ba sai su saki macce.

Na biyu kuɗi, ana zargin cewa wasu dattawan suna samun nasarar auren ƙaramar macce ne kyakkyawa saboda kuɗinsu.

Na ukku sarauta ita ma ana hasashen tana ɗaya daga cikin abubuwan dake jawo hankalin ƴan matan auren dattawan.

A wani labarin kuma

An Ɗaura Auren Sirri Mata Ta 2 Ga Maimartaba Sarkin Kano

Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya auri mata ta biyu, Hauwa’u Adamu Abdullahi Dikko.

An ɗaura auren ba tare da taron jama’a ba a ranar Juma’a a gidan marigayi Jarman Kano, Farfesa Isah Hashim, da ke unguwar Nassarawa G.R.A a Jihar Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa amaryar ta fito ne kai daga zuriyar Malam Jamo, wanda dan uwa ne ga marigayi Sarkin Kano, Ibrahim Dabo.

An fara batun shirye-shiryen auren tsakanin Sarkin mai shekara 60 a duniya da kuma tsohuwar masoyiyarsa a shekarar da ta gabata.

An bayyana cewa sarkin ya auri mace daya ne sama da shekara 30 kuma suna da ‘ya’ya hudu a tsakaninsu.

Madakin Kano, Alhaji Yusuf Nabahani Ibrahim, ne ya wakilci ango a matsayin waliyyi a wajen daurin auren, yayin da Alhaji Shehu Hashim, ya kasance waliyyin amarya.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa Majiyar Focus News Hausa, Aminiya cewa an biya Naira 500,000 a matsayin sadaki kuma an kai amarya gidan mijinta a ranar Asabar.

“An daura auren ba tare da sanarwa ba. Ko da yake sarki ya yi gaggawar dawowa daga Maroko. An kai amarya Fada a ranar Asabar.”

Aminiya ta ruwaito cewa Makaman Bichi, Alhaji Isyaku Umar Tofa, Sarkin Dawaki Mai Tuta na cikin wadanda suka halarci daurin auren.

Views: 32

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *