Ko kun san cewa a yau 9/01/2023 an fara dokar kayyade fitar da garin kudi (CASHLESS POLICY) wadda take hana kowane mutum ɗaya (Individual) ya cire kuɗi da suka haura ₦500,000 a kowane mako, sannan ga kowane asusun kamfani “Corporate Account” ba shi da ikon fitar da sama da ₦5,000,000!!! In kuwa har kuna son cire sama da haka dole sai kun bi wasu LONG PROCEDURES masu wahala ciki har da COURT ORDER da sa hannun alkali da D.P.O bayan an maku tambayoyi an gamsu da abin da za ku yi da kudin, sannan kuma duk da haka sai an cire maku harajin 5% daga cikin kudin da kuka cire
TO GA SHAWARA:
Na san dai mafi yawancinku a sana’arku ta POS, musamman ‘yan kananan masu POS irina da wuya idan kuna cire kudin da ya kai miliyan biyar (₦5,000,000) a kowane mako!! To me zai hana kawai ku bude CORPORATE ACCOUNT da sunan kamfaninku ko kasuwancinku?
Akwai ka’idoji da ake bi domin bude Corporate Account, ga su kamar haka:
- Dole ne sai kamfaninku/kasuwancinku yana da rajistar CAC, don haka dole ne sai kun yi wa sana’arku rajista, hakan kuwa zai chaje ku wasu ‘yan kudi a da za su kai 20,000 ko sama da haka.
- Wani karbabben ID Card na gwamnati (National ID Card, Voter’s Card, or Driver’s License, etc).
- Takardar Biyan Wuta (Nepa Bill) ko ruwa (Water Bill).
- Passport Photograph
- 2 Refs (Watau wasu mutum biyu wadanda suke yin amfani da CORPORATE ACCOUNT), wannan ko mutum daya ma ka kai masu za su yarda da shi.
- Kudin bude asusun ₦10,000.
Idan ka lura za ka ga cewa, za ka dan kashe wasu kudi yayin bude asusun, amma ka sani cewa hakan zai fi maka sauki a cikin wannan yanayin na dokar CASHLESS POLICY domin za ka rinka samun kudin da za ka yi business dinka cikin kwanciyar hankali ba tare da kudi yana maka karanci ba, kuma ma cikin kwana nawa ne za ka maida kudin in dai kana samun harka sosai?
Sannan ka sani cewa, shi wannan asusun CORPORATE ACCOUNT idan ka bude kuma business dinka yana da rajista da CAC, to za ka rinka samun damar karbar bashi daga gwamnati gwargwadon jujjuyawar kudi a cikin asusun naka wanda za ka yi amfani da shi domin haɓɓaka kasuwancinka.
Don haka me kake jira?
Maza ka garzaya ka yi rajistar business dinka da CAC don ka bude CORPORATE ACCOUNT ka ci gaba da sana’arka ta P.O.S hankali kwance ba tare da yankewar CASH yana ba ka tangarda ba.
Views: 35
