Kwankwaso Ya kaddamar da kwamitin Yakin Neman zaben sa yau a Abuja.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, PhD, FNSE da mataimakinsa dan takarar shugaban kasa Bishop Isaac Idahosa sun kaddamar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na NNPP wanda ya gudana a Abuja.
A jawabinsa na bude taron, Sanata Kwankwaso ya bukaci daukacin ‘yan majalisar da su jajirce wajen ganin jam’iyyar ta samu nasara a zaben 2023 mai zuwa. Ya godewa dukkan abokansa da suke aiki a bayan fage domin shirya taron tara kudade ga jam’iyyar tare da godewa daukacin ‘yan Najeriya bisa goyon bayan da suke bayarwa.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP shine shugaban kwamitin sannan Folashade E. Aliu zata kasance sakatariyar yakin neman zaben jam’iyyar PCC ta kasa.
📷Saifullahi Hassan
Dama dai an jima ana ta cece kauce kan cewa Kwankwason ya ƙi mayar da hankali wajen fara yaƙin neman zaɓensa ganin cewa sauran manyan jam’iyyun siyasa a ƙasar irin su APC da PDP tuni sun yi nisa wajen fara gudanar da yaƙin neman zaɓensu.
Ana sa ran Kwankwaso zai fara ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen nasa ne a jihar Rivers kamar yadda aka bayyana gabanin babban zaɓen ƙasar na wannan shekara ta 2023
Views: 9
