TikTok wata manhaja ce dake zama ɗaya daga cikin waɗanda suke kan gaba wajen tarin mabiya a tsakanin shafukan sada zumunta na zamani wato Social Media.
Manhajar TikTok na ɗaukar hankalin ƴan Najeriya ƙwarai dagaske inda wasu ke amfani da ita wajen isar da saƙon daya dace yayin da wasu kuma ke sheƙe ayarsu suna sharholiya a baya bayannan an nuno wani matashi yana sumbatar wata budurwa baki da baki abinda yasa wasu ki kiranyen ya kamata a rufe shafin TikTok ɗin a Najeriya ganin cewa babu abinda aka yaɗawa face alfasha.
Tuni dai ɗaiɗaikun mutane ƴan ƙasa da ma malaman addinin Musulunci suka yi tur da irin bidiyoyin da masu amfani da safin na TikTok suke yaɗawa yayin da wasu ke roƙon hukumar sadarwar Najeriya ta toshe kafar kamar yadda ta toshe shafin Twitter a shekarar 2021
Ga rubutun wani matashi shima wanda ya fara da.
Innallahi wainna Ilaihi Raji’un
Maganar Gaskiya Matsala Ta Ƙaru a TikTok
Yanzu haka an fara yaɗa fina-finan runguma da Kiss tsakanin mata musulmai da maza a manhajar TikTok.
Idan har shugabanni basu tashi tsaye sun yaƙi wannan baɗala ba, wallahi hakan ba ƙaramar illa bace ga tarbiyyar yara masu tasowa musamman a Arewa.
Allah ya kyauta
Daga Malam Salisu Na Annabi
Views: 7
