Yanda a ka ci tarar Firayim Ministan Burtaniya saboda rashin sanya bel ɗin kujera a mota.
‘Yan sandan Lancashire sun ci tarar Firayim Ministan Burtaniya Rishi Sunak saboda kasa sanya bel a bayan motar da ke tafiya.
Sunak, wanda ya yi rikodin bidiyo na Instagram a makon da ya gabata yayin da yake tafiya zuwa Arewacin Ingila, an gan shi yana juya kan kujerarsa don yin magana da kyamara ba tare da bel ɗin kujera ba.
A cikin faifan bidiyon, an ga firaministan yana jawabi ga ‘yan kasar kan yadda yake cika alkawarin da ya dauka na bunkasa tattalin arzikin kasar Burtaniya ta hanyar Asusun Tallafawa.
Views: 20
