PDP na zargin Masari da shirin kashe Naira Miliyan 500 don tarbar Buhari
Jam’iyyar adawa ta PDP a Jihar Katsina, ta zargi Gwamnan Jihar, Aminu Bello Masari, da bayar da umarnin kashe sama da Naira miliyan 500 daga asusun kananan hukumomin jihar don tarbar shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa jihar.
Ana sa ran Buhari zai kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu, daga ranar 26 zuwa 27 ga watan Janairu a jihar.
LEADERSHIP Hausa ta rawaito cewa jam’iyyar adawa ta PDP a jihar ta soki wannan shiri, inda ta alakanta da shi a matsayin almubazzaranci.
Shugaban kungiyar yada manufofin Atiku da Lado, Alhaji Lawal Ɗan Ade ya yi zargin cewa za a kashe kudaden ba bisa ka’ida ba.
Alhaji Lawal Dan Ade, ne ya shaida wa manema labarai cikin wata takarda da ya ce gwamnan jihar, ya amince tare da sahale kashe kudaden.
Views: 19
