Labari Da Ɗumi Ɗumi: “CBN ya bada kai bori ya hau”

Babban bankin Najeriya CBN zai duba yiwuwar ƙara wa’adin amfani da tsoffin kuɗin ƙasar kamar yadda wasu rahotanni ke bayyana cewa gwamnan babban bankin Godwing Emefiele.

Na shirin jagorantar daraktocin manyan bankunan ƙasar don cimma matsaya.

Idan an zaɓe ni zan share wa ƴan Nijeriya hawaye kan canjin kuɗi

Ɗan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar NNPP, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce zai share wa ƴan Nijeriya hawaye idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.

Kwankwaso ya kuma ce ba ya goyon-bayan tsarin da aka bi wajen sauya takardun kuɗi a Najeriya.

Kwankwaso da ke shaida hakan a lokacin wata tattaunawa da BBC, ya ce yanzu abu guda shi ne mahukunta a kasar su kokarta su kara wa’adin da babban bankin kasar ya bayar na daina amfani da tsoffin takardun kuɗi.

Injiniya Kwankwanso ya ce al’umma na shan wahala sakamakon canjin kuɗin, don haka ya kamata gwamnati ta sassauta

Kalaman ɗan takaran na zuwa ne kwanaki kadan wa’adin da babban bankin Najeriya wato CBN ya bayar na daina karban tsoffin kuɗi ya cika.

Sai dai dɗn takarar ya ce idan gwamnatin APC mai Mulki ta ƙi kara wa’adin, kada kowa ya ta da hankalinsa.

Injiniya Kwankwaso ya ce masu kuɗi su ajiye kudinsu, idan ya samu nasarar zama shugaban kasa zai bai wa kowa damar canja kuɗinsa ba tare da kwabonsa ya yi ciwon kai ba.

Views: 44

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *