RA’AYI RIGA:
Tunubu Zai Iya Mulkin Najeriya Ko Babu Man Fetur—Abdullahi Adamu
Wani matashin ɗan siyasa a jihar Yobe Abdullahi Adamu Ɗanjuma ya yi kira ga ƴan Najeriya da su fito ƙwan su da ƙwarƙwata su zabi ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC Bola Ahmad Tunubu.
Matashin ya kafa hujja da cewar Alhaji Bola Ahmad Tunubu zai iya tafiyar da mulkin Najeriya cikin ƙwarewa ko da kuwa babu man Fetur a ƙasar kamar yadda ya gudanar da mulkinsa a lokacin da yana Gwamnan jihar Legas daga shekara ta 1999-2007 tsawon shekaru 8 da ya shafe yana mulkin jihar ta Legas.
Ba’a taɓa binsa bashin albashin ma’aikata ba kuma har ya bar mulki ba a bin jihar Legas bashin ko sisin kobo sannan ya yi ayyukan ci gaba sosai a jihar ba tare da ya dogara da gwamnatin tarayya ba don kuwa akwai lokacin da ba’a turo masa kuɗi daga gwamnatin tarayya ba wato Grant amma a haka ya yi amfani da ilimi da ƙwarewarsa wajen samo hanyoyin da ya tara kuɗaɗen shiga ba tare da ya ƙuntatawa talakawan jihar ba.
Sannan ina kira ga al’ummar jihar Yobe su zaɓi mai girma Gwamnan Hon. Mai Mala Buni a karo na biyo ganin yadda ya gudanar da ayyukan raya ƙasa a jihar mu ta Yobe kowa sai san barka yake yi.
Bugu da ƙari ina jin jina wa shugaban jam’iyyar APC na jihar Yobe bisa jajircewa da ƙoƙarinsa ba dare ba rana don ganin jam’iyyar ta samu nasara a dukkan matakai tun daga Shugaban ƙasa zuwa Gwamna da Sanatocinmu guda ukku da ƴan majalissu.
Ina fatan Allah ya ba jam’iyyar mu ta APC nasarar lashe zaɓen Shugabancin Najeriya da kujerar gwamnan jihar Yobe da sauran kujeru ameen.
@Abdullahi Adamu Ɗanjuma Youngest Politician Yobe State
Views: 15
