Yadda mijina ke nuna ɓacin rai da zarar tusa ta kuɓuce min a gabansa—Matar Aure

Yadda mijina ke hassala tare da nuna ɓacin rai da zarar tusa ta kuɓce min a gabansa.

Wata mata ta shiga damuwa bayan da tusa ta kubce mata a gaban mijinta inda ya nuna rashin jindadinsa karara duk da sun kwashe shekaru 9 da aure,.

Ta shaida yadda take shiga tararrabi da zarar ta ci wani abu wanda zai iya ɓata mata cikinta. Hakan yasa take matuƙar kiyayewa.

Matar ‘yar kasar Australia, Emma ta bayyana cewa:

“Mijina, Rob ba ya iya yafe min sannan yana nuna kyamarsa a fili tare da gwada min cewa ba halin mata bane da zarar na saki tusa a gabansa duk da abokansa na nuna masa ba daidai bane.”

Emma ta sanar da Kidspot cewa ta san Rob yana tsanar mata da zarar sun yi tusa, kuma tsawon shekaru 9 da suke tare tana iyakar kokarin ganin ta kiyaye yi a gabansa.

Ta ce da zarar ta saki tusa bisa kuskure ko kuma ta ci Pizza ta yi bacci, za ta dinga sakin tusa babu kakkautawa.

Emma ta ce ita da Rob suna yin komai a gaban juna, banda tusa. Ta ce ko da kuwa tusar bata yi wari ba, sai ya dinga korafi. Ya fi son ta shiga bayi ta rufe kan ta ta saki.

By _Dimokuraɗiyya.com_

Views: 63

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *