Dan takaran shugaban kasa karkashin jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), Senator Rabiu Musa-Kwankwaso, ya yiwa yan Najeriya alkawarin share musu hawaye idan ya hau mulki.
Kwankwaso ya ce zai soke tsarin sauya fasalin Naira, zai magance matsalolin tsaro kuma ya dakile yunwa.
Tsohon gwamnan jihar Kanon ya bayyana hakan ne yayin jawabi ga dubunnan masoya jam’iyyar NNPP a garin Funtua, jihar Katsina, rahoton ThisDay.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yiwa yan Najeriya alƙawurra guda 3 masu muhimmanci Saura kwanaki biyu yan siyasa su kammala kamfe kamar yadda dokar zabe na INEC ta bukata.
Kwankwaso na cikin manyan yan takara hudu a zaben shugaban kasa da zai gudana ranar Asabar.
Dan takaran shugaban kasa karkashin jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), Senator Rabiu Musa-Kwankwaso, ya yiwa yan Najeriya alkawarin share musu hawaye idan ya hau mulki. Kwankwaso ya ce zai soke tsarin sauya fasalin Naira, zai magance matsalolin tsaro kuma ya dakile yunwa. Kwankwaso zai fafata da sauran yan takara ranar Asabar, 25 ga Febrairu, 2023.
Tsohon gwamnan jihar Kanon ya bayyana hakan ne yayin jawabi ga dubunnan masoya jam’iyyar NNPP a garin Funtua, jihar Katsina.
Kwankwaso Ya bayyana cewa zai amince yan Najeriya su mayar da dukka tsaffin kudinsu banki idan yayi nasara. Ya yi bayanin cewa wannan tsari na bankin CBN zai sakejefa yan Najeriya cikin mangin talauci duk da cewa yanzu haka akwai mutum milyan 33 da ke fama da bakin talauci. Yace:
“An fada mana cewa akwai yan Najeriya milyan 133 amma suka kawo sauyin fasalin Naira a wannan lokaci mai muhimmanci na zabe. Wannan tsari ya jefa talakawa da dama cikin kunci, yunwa, wahala. “Amma idan kuka zabeni matsayin shugaban kasar nan tare da sauran yan takaran NNPP, mun yi alkawarin kawo karshen wannan doka kuma zamu bari ku kai tsaffin kudadenku bankuna don ajiya ko harkokinku.”
“Mu a NNPP na shirin yiwa yan Najeriya mulkin kwarai, samar da zaman lafiya, magance tsaro, da inganta tattalin arziki.” Ya ce jam’iyyar NNPP na da ikon kawo karshen rashin tsaro a fadin kasa.
Source: Legithausa
Views: 5
