INEC Duk wanda ya aika waɗannan laifuka wajen zaɓe zai biya tarar ₦500,000 ko sama da haka

INEC Duk wanda aka kama ya aika waɗannan laifuka wajen zaɓe zai biya tarar ₦500,000 ko sama da haka

1 Ba’a yaƙin neman zaɓe ranar zaɓe. Ba’a so wani yafi to da fesin kaf, ko mota mai ɗauke da hoton ɗan takara ko waƙa a lokacin da ake gudanar da zaɓe.

2 Ba’a zuwa da alamar jam’iyya ko ta ɗan takara rumfar zaɓe.

3 Ba’a zaɓe da katin wani. Ba’a zuwa da katin da ba naka ba, misali wani ɗan’uwan ka da ya rasu.

4 Ba’a zaɓe a rumfar da ba’a nan akayi rijista ba. Ba’a son mutum yaje rumfar zaɓen da ba tasa ba. Idan aka kama mutum za’a ci tarar sa ₦100,000. Ko wata 6 a gidan yari.

5 Ba’a tashin hankali ko tilasta wa masu zaɓe. Ba’a so mutum yazo wajen zaɓe ya tada wa mutane hankali, cewa sai dai ku zaɓi wane, shima ya saɓa ma doka. Idan aka kama mutum zai biya tara ₦500,000 ko wata 12 gidan yari

6 hana kai hari kan jami’ai da kayan zaɓe. Idan aka kama ka zaka biya tara ₦1,000,000 ko kuma shekara 3 gidan yari.

Source by INEC na shekarar 2022 sashe na 123 zuwa na 128.

Views: 12

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *