HOTUNA: “An kaiwa waɗanda suka tafi tarban Kwankwaso hari a Na’ibawa.”

Jirgin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar New Nigeria Peoples Party NNPP, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso Zai Sauka Tasha Yau A jihar Kano.

Kwankwaso wanda ya mulki Kano har sau biyu zai karkare kamfensa a mahaifarsa.

Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa ya dira jihar Kano lafiya kuma ya ya’da zango karamar hukumar Bebeji inda ya samu tarbar dinbim mabiya.

Kwankwaso ya yi kira da mabiyansa kada su tanka ma masu tada tarzoma kuma su bi doka da oda.

A jawabin da ya daura a shafinsa na Tuwita yace:

ku latsa wannan Link domin gani da ido

RMK 2023

“Mun biya garin Kofa dake karamar hukumar Bebeji yayinda muke hanyarmu ta zuwa Kano.
“Soyayyar da aka nuna mana gagaruma ce. Ina kira ga mabiya su kasance masu bin doka yayinda za’a cigaba da taro,”

Rahotanni sun yawaita kan cewa wasu yan daba sun kai wa masoya Kwankwaso hari yayinda suke hanyar zuwa tarban dan takarar shugaban kasa.

Hotuna sun nuna yadda aka kona motoci masu dauke da hotunan dna takarar.

Har yanzu ba’a ji komai daga bakin hukumar yan sandan jihar ba.

Source: legit.ng Hausa

Views: 28

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *