Za a samu ƙaruwar masu teɓa nan da 2035

Za a samu ƙaruwar masu teɓa nan da 2035′

Ƙungiyar da ke yaƙi da matsalar teɓa ta duniya ta ce nan da shekarar 2035, za a bayyana sama da rabin al’ummar duniya ko fiye da mutane biliyan huɗu a matsayin masu teɓa.

A sabon rahotonta, ƙungiyar ta ce adadin mutanen na ƙaruwa musamman a tsakanin yara – sannan kuma galibin ƙasashen da ake hasashen za su fuskanci ƙaruwar masu teɓa cikin shekara 12 masu zuwa za su kasance daga matsakaita ko ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi a Afirka da Asia.

Ƙungiyar ta ce nan da shekarar 2035, kuɗin kula da teɓa zai kai dala triliyan huɗu duk
shekara inda kuma ta buƙaci gwamnatoci da su ɗauki mataki.

Source: bbchausa

Views: 35

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *