Wani Dan Sanda Ya Harbe Budurwarsa Har Lahira Shima Ya Kashe Kansa
Yan sanda a jihar Kwara na gudanar da bincike kan kisan gillar da wani dan sanda ya bindige wata mata har lahira a harabar wata makaranta ranar Alhamis a Ilorin.
Dan sandan ya kuma harbe kansa har lahira bayan ya yi kisan.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa An yi imanin matar da aka kashe budurwar dan sandan ce.
Wani ganau ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa, bayan isowar matar da yaronta makaranta, jami’in ‘yan sandan ya kama matar da aka kashe, inda suka tattauna da ita kafin ya harbe ta har sau biyu.
Ya kara da cewa nan take ɗan sandan ya harbe kansa har lahira.
Wani ganau da ya ga lamarin daga wani gini da ke kusa ya tabbatar da faruwar lamarin.
Wani magidanci da ke ikirarin cewa shi mai kadarorin ne ya ce dan sandan da matar sun dauki hayar wani gida a wurinsa makonnin baya kuma sun kasance kamar tsuntsayen soyayya har suka fara samun matsala tun kwanaki biyar da suka wuce.
“Suna da matsala tun kwanaki biyar da suka gabata. Tun sa’ad da suka karbi hayar gidan, muna jin daɗin yadda suke nuna ƙauna ga juna.
Wasu sun ce dan sandan abokin matar ne, amma sun yi ta rigima tun ‘yan kwanakin da suka gabata,” in ji mutumin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, SP Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da cewa wani dan sanda ya kashe wata mata da kansa ranar Alhamis a Ilorin.
Ya shaida wa majiyar DIMOKURADIYYA cewa yayin da bayanai ke ci gaba da bayyana, an gaya masa cewa lamarin soyayya ya yi tsami.
Okasanmi ya ce ‘yan sanda sun fara bincike kan lamarin. (NAN)
Source: dimokuraɗiyya
Views: 4
