Dan aikin gida ya yankewa tsohuwa farjinta domin yin tsafin da zai samun kudi

Dan aikin gida ya yankewa tsohuwa farjinta dan yin tsafin samun kudi

Lamarin ya farune a jihar Anambra.

Dan aikin me suna Onyebuchi Ezeh ya yanke al’aurar wata mata me shekaru 72 da sauran wasu sassan jikinta dan gudanar da tsafi na samun kudi.

Lamarin ya farune a kauyen Umunze, dake karanar hukumar Orumba ta jihar.

An garzaya da tsohuwar Asibiti inda kuma aka kama dan aikin gidan kuma ya amsa laifinsa.

Yace wani bokane yace su kai masa sassan jikin dan Adam dan gudanar da tsafi.

Yanzu haka dai wanda ake zargi na can hannun ‘yansanda ana bincike, kamar yanda Punchng ta ruwaito.

Source: hutudole.com

Views: 5

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *