Wata budurwa ‘yar shekara 17 ta rasa hannu da ƙafa sakamakon yi mata auren dole

Wata yarinya ‘yar shekara 17 da aka yi mata auren dole ta rasa hannunta da kafa bayan mijinta ya kai mata hari da adda a Kebbi.

Jami’an gwamnatin jihar sun shaida mata cewa tuni aka kai rahoton faruwar lamarin ga ‘yan sanda.

Wata yarinya ‘yar shekara 17 mai suna Malama Hauwa Mohammed ta rasa gabobinta biyu.

Hakan ya biyo bayan wani mummunan hari da mijinta ya kai mata a gidansu dake jihar Kebbi.

A cewar Hauwa, ta yi aure da mijinta ba tare da so ba. Ta ce mijin nata yana da dabi’ar zama a gida ko da yaushe tsawon watanni. Sai dai a ranar da aka kai harin, ya isa gida da adda, ya kai mata hari ba tare da nuna damuwa ba.

Hauwa ta bayyana hakan ne ga mambobin kungiyar Technical Working Group kan cin zarafin mata ta jihar da suka kai mata ziyara a cibiyar kula da lafiya ta tarayya dake Birnin Kebbi inda take jinyar raunukan da ta samu.

Jami’an gwamnatin jihar sun shaida mata cewa tuni aka kai rahoton faruwar lamarin ga ‘yan sanda kuma da zaran an kama wanda ya aikata laifin za a gudanar da bincike don gano musabbabin abin da ya aikata kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu.

Source: torinews
From Opera News

Views: 65

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *