DALILAN DA YASA BAI KAMATA A ZABI ABBA GIDA-GIDA GWAMNAN KANO BA
DAGA Datti Assalafy
(1) Kwankwaso ya tara magoya baya marassa tarbiyya masu jifan kowa da manyan buhunnan ashariya, kalilan ne masu halin Dattako a cikinsu
(2) Mafi yawan ‘yan Kwankwasiyya basa ganin girman kowa a Kano da Nigeria imba girman Kwankwaso ba, zasu iya keta mutuncin kowa akan Kwankwaso
(3) Akwai alamun Dabanci da kwacen wayoyi zai karu sosai a Kano
(4) ‘Yan nanaye da ‘yan daudu da masu lalata tarbiyya zasu samu gurbin zama da cikakken ‘yanci a Kano
(5) Rashin kunya da cin mutuncin Malamai tare da yin fito na fito da Malamai zai karu sosai a Kano
(6) Zasu lalata Masarautun Kano, watakila su dawo da mai akidar feminist da aka kora kan kujeran Mulki
(7) Da akwai yiwuwar kubutar da Abduljabbar jagoran masu cin mutuncin Manzon Allah (SAW) a Kano
Kanawa kuyi taka tsantsan sosai, kar ku yadda ku zabi Abba Gida-Gida, ku zabi Dr Gawuna ko Sheikh Ibrahim Khalil
Muna kaunar Kano kamar yadda muke kaunar garuruwan mu na Arewa saboda Kano itace cibiyar Arewa, duk abinda ya taba Kano ya taba mu
Muna fatan Allah Ya tabbatar da alheri
source: Hausa linzami facebook
Views: 30
