Ƴan sanda sun kama mutane 5 masu tono gawar mutane suna siyar wa

  • Yan sanda sun kama wasu mutane biyar kan safarar sassan jikin bil adama a garin Ijebu a jihar Ogun
  • Rundunar yan sandan ta ce mutane biyar din da aka kama a Ijebu sun amsa cewa suna sayar da sassan jiki ga masu asiri
  • Frank Mba, kwamishinan yan sanda ya tabbatar da lamarin yana mai cewa an tura binciken sashin binciken manyan laifuka.

Jihar Ogun – Rundunar yan sandan Najeriya reshen jihar Ogun ta kama wasu masu asiri da ke mummunan sana’arsu a Ijebu ta jihar Ogun.

Wadanda ake zargin sune: Oshole Fayemi, dan shekara 60; Osemi Adesanya dan shekara 39; Ismaila Seidu, dan shekara 30; Oseni Oluwasegun, dan shekara 69 da Lawal Olaiya, dan shekara 50.

Tawagar mutanen biyar – wadanda ake zargin cewa sune suka hako gawarwaki a Ososa – yankin Ijebu kuma suka cire sassan jikinsu domin yin asiri, an kama su yayin da suke shirin sake zuwa hako wasu gawarwakin a garin.

An gano cewa DPO na Odogbolu, CSP Godwin Idehai, ya samu bayanan sirri, hakan yasa ya tattara mutanensa suka kai farmaki mabuyar wadanda ake zargin kuma aka kama su.

source: legit.ng

Views: 13

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *