VIDEO:An kama wasu Maza 3 bisa zargin yin Jima’i da Matar Aure da cewar zasu bata Ɗariƙa

VIDEO:Yadda matasa guda 3 suka yi Jima’i da matar Aure da niyyar zasu bata Ɗariƙa.

Samarin sun haɗa da Rufa’i Salisu, Tukur Ɗan Azumi, Abubakar Yahuza.

Matar mai suna Zainab Ahmad ƴar kimanin shekara 22 da take zaune a Unguwar Ɗan Talle dake ƙaramar hukumar Ɗanja a Jihar Katsina.

Ta bayyana cewar; taje wajen matasan ne domin ta karɓi Ɗariƙa inda kuma suka bata ɗariƙar, sai dai sun kafa mata wani sharaɗi na cewar dole sai sun sadu da mace sannan ake samun karɓuwa a Ɗariƙar.

jin hakan ne yasa Zainab Ahmad ta amince kuma tayi jima’i da samarin guda uku domin ta samu karɓuwa a ɗariƙar da ta amsa.

Samarin sun haɗa da Rufa’i Salisu, Tukur Ɗan Azumi, Abubakar Yahuza.

Abubakar Yahuza ya ƙara da cewar sunan ƙungiyar tasu”HAƘIƘA” kuma su ƴan Faira ne suna zikiri da wazifa a majalisar su.

Source:jakadiyar arewa tv2 Instagram

Views: 20

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *