Daga yanzu babu maganar sulhu na baku wa’adin sa’a 24 ku ceto daliban Islamiyar da aka sace—Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bada umarnin ceto daliban Islamiyar da aka sace a jihar Neja.

A yanzu ba maganar sulhu bace, ina umurtar jami’an tsaro da su gaggauta ceto dalibban makarantar Islamiyya da aka sace a Neja~ Inji Buhari

A wannan karo, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya murji gashin baki ya umurci jami’an tsaro da su gaggauta kai farmaki ga ‘yan bindigar da suka sace dalibban makarantar Islamiyya ta Salihu Tanko dake Tegina jihar Neja.

Yawan dalibban wadanda ake kyautata zaton sun kai su 200, shugaba Buhari ya umurnci jami’an tsaro da su gaggauta ceto su.

Kuma wannan dai shine karo na farko da shugaba Buhari ya murji gashin baki ya bada umurni irin wannan.

Muna fatar Allah yasa jami’an tsaro su yi nasarar ceto wadannan dalibbai cikin ruwan sanyi ameen.

Daga Nasara
Media News

Views: 54

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *