An gurfanar da RARARA a gaban wata kotun shari’ar Muslunci dake Kano, ana zarginsa da cinye kuɗin wani mutum Naira Miliyan 10
An gurfanar da shahararren Mawaƙin jam’iyar APC Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu(Rarara) a gaban babbar kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta a Unguwar Rijiyar Zaki Kano, ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Halhaltul Khuza’i Zakariya.
Tunda fari wani mai suna Muhammad Ma’aji ne ya maka Rarara agaban kotun kan wasu kuɗaɗen sa Naira Miliyan 10 da suka ƙulla wata harka a watannin da suka gabata.
Mai ƙarar ya shaida wa kotun cewa, bashi da wani zaɓi dan ya ƙarɓi haƙƙinsa sai ta fannin shari’a kamar yadda kowa yake da ƴan cin shigar da ƙara kan hanashi haƙƙinsa.
Muhammad Ma’aji ya ƙara da cewa ya bi matakin sulhu da wanda yake ƙara dan ya bashi kuɗin sa tunda dai harkar bata yiwu ba kuma yaƙi bashi kuɗinsa.
Kakakin manyan kotunan shari’ar Addinin musulinci na jahar Kano Muzammil Ado Fagge , ya bayyana cewa , za a fara sauraran ƙarar a ranar 11 ga watan Afrilun 2023.
” wannan ƙara ce wadda , Muhammad Ma’aji ya shigar da Rarara Mawaƙin APC kuma ƙara ce wadda akwai mu’amulla dashi har ta naira miliyan 10 kuma ya yi , ya bashi ƙuɗin amma yaƙi” Muzammil A. Fagge”.
Shafin yanar gizo na Oddity24 ya ruwaito cewa kakakin manyan kotunan shari’ar addinin muslincin na jahar Kano, ya ce sun yi amfani da doka ta Oda 9 2021 da ta yi magana cewa idan aka nemi mutum dan abashi sammaci ba aganshi ba to za a iya yin amfani da shafukan sada zumunta dan sanar da shi ko kuma a liƙa
masa a gidan sa.
” shi wannan Mawaƙin sai wasan buya yake yi da jami’in mu dan ya bashi sammacin amma yaƙi yadda su haɗu , shi yasa muka nemi mai unguwarsa da kuma shaidu muka liƙa masa a gidan sa dake Zooroad
Views: 17
