Yadda wata budurwa baturiya tayi tattaki daga Amurka zuwa Najeriya tayi wuff da wani saurayi.
Wata dattijuwar mata da ke zama a Amurka ta haddasa cece-kuce bayan bayyanar bidiyonta tana auren wani dan Najeriya.
Matar, wacce ke cike da farin ciki da tafiyar, ta yi shar da ita a wani hadadden doguwar riga a lokacin aurenta.Mutane da dama a sashin sharhi sun taya ta murna yayin da suke fatan hakan zai zamo mafi alkhairi ga ma’auratan.
Wacce ke zaune a Amurka, ta yi dan gajeren bidiyo da ke nuna lokacin da ta garzaya Najeriya don auren sahibinta.Ta dauki bidiyon kanta a cikin jirgin sama yan mintuna kafin su sauka.
Yan sakanni a bidiyon, matar ta kasance cikin farin ciki sanye da doguwar rigar amare.Ma’aurata a wajen shagalin bikinsuWata Dattijuwar Mata Ta Yi Tattaki Daga Amurka Zuwa Najeriya, Ta Yi Wuff Da Matashin Saurayi Shagalin bikin aure me kayatarwa.Wani bangare na bidiyon ya nuno dangin mutumin kewaye da ita yayin bikin aurensu. Dan karamin taro ne amma mai matukar tasiri.
A wallafar da ta yi, ta bayyana cewa ta yi matukar farin ciki da auren mijin nata.Mutane da dama sun je sashin sharhi na matar domin taya ma’auratan murna. Wasu sun gargadeta kan fitar da mutumin kasar waje cikin gaggawa.Source: Hausa.legit.ng
Views: 24
