Turancina bazai bani damar nayi magana da yaren Turanci ba sai dai nayi da Hausa —Bazoum

A ranar 24 ga watan Mayu ne aka gudanar da bikin ɓuɗe katafariyayar Matatar man Fetur da Shahararren ɗan kasuwar Afrika wato Alhaji Aliko Ɗangote ya gina a Lekki Dake Jihar Lagos.

Taron ya samu halartar shuwagabannin ƙasashen Afrika guda Shida cikin su harda Shugaban Najeriya Muhammad Buhari da Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum da sauran shuwagabannin guda huɗu.

Babban abinda ya baiwa mutane mamaki da kuma burge wa shine; yanda Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum yayi jawabi da harshen Hausa duk da taron ya haɗa da manyan shugabannin ƙasashen Afrika da basu Amfani da harshen Hausa.

ku shiga Nan domin kallon cikakken bidiyon shugaban kasar Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum yayi Jawabi da Harshen Hausa a wajen taron buɗe matatar man Fetur ta Ɗangote 👇👇👇

https://www.instagram.com/reel/CslLh7FLO5F/?igshid=NTc4MTIwNjQ2YQ==

Views: 8

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *