1- Zata rage jin kunyarka da kaso 40%
2- Maganar da bata iya fada maka a baya, yanzu zata dinga fada maka,
3- Hatta wani ciwo da take fama dashi, wanda a duniya in ba iyayenta ba, babu wanda yasan da wannan ciwo, a yanzu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali zaka ji tana labarta maka shi,
4- Abinda bata iya tambayarka a baya, yanzu ko gezau ba zata yi ba wajen tambayarka,
5- 70% na firarku a yanzu zaku dinga yinta ne akan rayuwar ku ta bayan an daura muku aure,
6- Dukkan abinda tayi a yanzu, ko akayi mata, ba tare da ka tambayeta ba zaka ji tana baka labarin sa!
7- Idan a baya kuna yin kwana 3 baku yi wayaba, to ka sani a yanzu zai zama laifi akanka kuyi kwana 2 ba tare da anyi waya ba,
8- Fada zai yawaita a tsakanin ku a yanzu, watakila a cikin kowanne sati daya sai kunyi fada a kalla sau biyu
Alakar Soyayya bayan sanya ranar Aure tana sauyawa, kamar yanda alakar Soyayya ke sauyawa bayan an daura Aure.
Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
Views: 37
