Inna lil Laahi maa akhaza, wa lahuu maa a’aɗa, wa indahuu kullu shai’in bi ajalin musammaa!
Haƙiƙa AuwalG Danbarno aboki ne na musamman wanda wannan kafa ta Facebook ta haɗa mu da shi, ƙarshe ya zama tamkar mun yi yarinta tare.
Mutum ne mai barkwanci, sannan mai fahimta idan ka masa bayani. Domin mun sha bugawa da shi, amma a ƙarshe mu wanye ba tare da cin zarafin juna ba.
Daga cikin wata ɗabi’arsa, idan ya ga wani ya yi kuskure, to zai kira wanda ya san zai iya yi wa wancan ɗin nasiha, domin ya nasihance shi.
Mun haɗu a wurare da dama, kuma duk haɗuwar alheri, sannan mu rabu cikin ɗoki da kewar juna.
Mutum ne mai son tattaunawar ilimi da bincike da son bayyana fahimtarsa, sai dai idan kana ƙalubalantarsa ka fito ka yi, idan ya ga gaskiyar, sai ya karɓa.
Maganarmu ta karshe idan ya dawo Kano za mu tattauna kan noma.
In sha Allahu za a yi jana’izarsa ƙarfe 4:00 a gidansa da ke Kurna.
Allah ya ji ƙansa, Ya haskaka makwanci, Ya sanya Aljanna makoma, Ya alkinta abin ya bari, Ya bai wa iyaye da iyali da dangi da abokai haƙurin wannan rashi, amin.
Ibrahim Garba Nayaya
Views: 9
