Yadda wata Budurwa ta yarda ta Mari Mahaifiyar ta akan kuɗi ₦2M
Wani bidiyo da ya yadu na budurwa da ta ce za ta iya marin mahaifiyarta ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.
A bidiyon da ya yadu, wani mutum ya tambayi budurwar kan ko za ta yarda a bata miliyan 2 don ta mari mahaifiyarta
Abun mamaki, ta yarda da bukatar harma ta yi alkawarin karawa a kan aikin idan aka biya ta kudin kamar yadda aka yi alkawari
Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jama’a sun yi cece-kuce bayan wani bidiyo na matashiya da ta yarda ta mari mahaifiyarta ya bayyana a dandalin TikTok.
Matashiyar budurwar ta bayyana ra’ayinta cike da karfin gwiwa bayan an bukaci ta mari mahaifiyarta kan naira miliyan 2.
Matashiya Ta Yarda Ta Mari Mahaifiyarta a Kan Miliyan N2
Tambayar ta bugeta sosai amma hakan bai sa ta karaya ba. Ta yi dariya da farko kafin ta bayar da amsarta cike da karfin gwiwa.
A cewarta, za ta mari mahaifiyarta a kan wannan makudan kudaden. Ta yi bayanin cewa mahaifiyar tata za ta fahimci lamarin kuma ba za ta dauki abun a zuciya ba.
Da take kare kanta, ta bayyana cewa tunda dai bata yi amfani da mahaifiyar tata wajen asiri (kudin jini) ba, toh mahaifiyar za ta karbi kudin a madadin marin.
Ta kara da cewar za ta yarda ta mari mahaifiyar tata sau 10 domin a kara mata kudaden.
Views: 9
