Ina gane matsalar Mota ne da zaran na saurari kukan ta — Makaho mai gyaran Mota

Ina gane matsalar Mota ne da zaran na saurari kukan ta — Makaho mai gyaran Mota

Wani bakaniken mota da ya makance sama da shekaru ashirin ya bai wa wani mutum mamaki da basirarsa ta gyaran mota.

Makahon da ke kanikancinsa a Abuja, ya ce zai iya gano matsalar da ke damun mota ta hanyar sauraron sautin injin kawai.

‘Yan Najeriya da dama da makahon ya birge sun ce yana buƙatar taimako, inda wasu suka yi ƙoƙarin janyo hankalin ‘Guinness World Records’ gareshi.

Abuja – Wani mutum ya sha mamaki kan yadda wani bakanike makaho ya gyara masa motarsa, hakan ya sanya shi ɗaukar hoton bidiyonsa, ya kuma yaɗa a kafar sada zumunta ta TikTok.

Makahon ya ce ya shafe shekaru sama da 30 yana kanikanci, sannan ya kuma bayyana cewa shekarunsa 28 kenan a matsayin makaho, inda ya ce hakan ya faru ne a lokacin da yake tuƙa mota.

bakanike makaho ya bayyana yadda yake gyaran mota
Makahon bakanike ya bayyana yadda yake gyaran mota.

Dalilin da ya sanya makahon ci gaba da aikin kanikanci.


Bakaniken ya ƙara da cewa ya zaɓi ya ci gaba da kanikancin ne saboda shi ne hanyar samun na abincinsa.

Bakaniken makahon ya kuma bayyana cewa yana iya gane matsalar mota ta hanyar sauraron sautin injinta.

Ya ce idan ya ɗauki sifana, yana iya gane girmanta duk da lalurar da yake da ita ta makanta.

Mai motar ya ce bai fahimci cewa bakaniken makaho ne ba ne sai da ya gama gyara masa motar ta sa.

A cewarsa:

https://apahausa.com.ng/video-ku-kalli-yadda-%c6%b4a%c6%b4an-hausawa-suka-lalace-zina-a-fili/

“Ina iya sanin matsalar mota ta hanyar sauraron sautin injinta, da zarar na riƙe sifana nake iya gane girmanta.”

Views: 17

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *