Yadda ake samun kuɗi ta internet Najeriya

“Yadda ake samun kuɗi ta internet Najeriya”

Yadda ake samun kuɗi ta internet a Najeriya ya zama ɗaya daga cikin hanyoyin samun kuɗin shiga da suka fi shahara a shekarar 2026. A wannan jagorar, za ka koyi hanyoyi masu sauƙi da ingantattu da za su taimaka maka fara samun kuɗi online cikin halal.

Yadda ake samun kudi ta internet Najeriya a cikin 2026

Akwai hanyoyin samun kuɗi ta Internet masu yawa sai wanda mutum ya zaɓa duk da cewar akwai na ƙarya akwai ma na damfara amma yau insha Allahu zan nuna muku hanyoyi kamar guda 3 da suke ingantattu.

https://apahausa.com.ng/allahu-akbar-%e2%82%a6aira-378681-kacal-buhari-ya-bari-a-asusun-sa-na-first-bank-olusegun-alebiosu/

Idan Facebook suka buɗe maka hanyar samun kuɗi ta subscription, ga yadda zakayi:

https://apahausa.com.ng/yadda-ake-samun-kudi-ta-internet-a-najeriya

/2lVaFpJy-zw?si=uBWdANoOJ9Znjn3d
  1. Kayi accepting
  2. Kayi setting payment information ɗinka (account number)
  3. Kayi selecting adadin kuɗin da mutane zasu biya kowane wata domin ganin postings ɗinka (N350 N500 N1000 N2000 N5000)

Bayan haka

/ekyZDZHK4Tk?si=UYOiiZu-SMOaqAGF

Idan kaje yin posting, wurin da ake saita audience zakayi selecting (subscribers) a maimakon (friends, public, ko followers)

Idan kayi wannan, sai wanda suka yi subscription ɗin page ɗinka zasu ga wannan posting

⚠️ ilimi mai muhimmanci shine yadace ayi subscribing

Kamar irin koyarda mutane hanyoyin samun kudi a yanar gizo, crypto, gyaran waya, ilimin kiwon lafiya, ilimin addini, da darussa masu muhimmanci wanda zasu amfane al’umma.

Ga Tambaya misali ga Adsterra zaka iya samun kudi dasu cikin sauki

https://beta.publishers.adsterra.com/stats

KA TAƁA FADAWA CIKIN ASARAR CRYPTO?

Daga Eng Muhammad Sunusi — Head of Media & Communications
NovaChain Blockchain Academy.

Yaushe za ka daina nadamar abin da ya faru da kai a duniyar Crypto? Yaushe za ka daina cewa, an cuce ni? Gaskiyar magana ita ce, rashin ingantaccen ilimi na daga cikin manyan dalilan da ke jefa mutane cikin matsaloli a wannan fage. Shi yasa aka kafa NOVACHAIN BLOCKCHAIN ACADEMY, domin taimaka maka ka fahimci Blockchain da Crypto daga tushe, cikin tsari mai kyau kuma a harshen Hausa.

A NovaChain, ba saka jari ko Mining zamu koya maka ba. Za mu taimaka maka ka fahimci ainihin yadda Blockchain da Crypto suke aiki, damammakin da ke cikinsu, da kuma ƙwarewar da zaka iya amfani da ita a wannan sabuwar duniyar fasaha. Zaku koyi yadda zaku gano da kuma nemowa kanku damammaki a duniyar Blockchain, ta hanyar ilimi da ƙwarewa, koda bakuda jarin ko kwabo.

Koda baka da wani ilimi game da Blockchain ko Crypto, ko kuma kana da ɗan ilimi kuma kana son ƙara zurfafa fahimtarka, akwai gurbin ka a NovaChain Blockchain Academy. Kana son sanin tsare tsaren wannan Academy? Ka ziyarci Telegram Channel ɗinmu domin samun cikakken bayani da kuma bibiyar duk abubuwan da ke gudana:

Muna maraba da zuwanku NOVACHAIN BLOCKCHAIN ACADEMY Inda Ilimi Ya Zama Farkon Tafiya.

YADDA AKE SAMUN KUDI TA INTERNET A NAJERIYA A 2026: HANYOYI 5 MASU SAUKI

Yadda ake samun kudi ta internet a Najeriya ya zama mafi sauki fiye da kowane lokaci. A shekarar 2026, dubban matasa na samun dubunnan Naira a kowane wata ba tare da sun fita daga gida ba. Idan kana da waya da data, kana iya farawa yau.

Ga hanyoyi 5 da aka tabbatar suna aiki a Najeriya:

  1. Facebook Monetization da Content Creation
    Wannan ita ce hanya mafi sauki a yanzu. Idan kana da shafin Facebook mai mabiya 5,000 da kuma views 60,000 a cikin kwana 60, Facebook zai bude maka hanyar samun kudi ta Ads on Reels da In-Stream Ads. Abinda zaka yi shine ka rika tura bidiyo na ilimantarwa ko labarai kamar na APA Hausa. Duk lokacin da mutum ya kalli talla a bidiyorka, Facebook zai biya ka dala.
  2. Affiliate Marketing (Tallan Kayayyakin Wasu)
    Kana iya yin rajista a Jumia Affiliate ko Amazon ko Expertnaire. Sai ka dauki link na wani abu kamar waya ko littafi, ka tura a WhatsApp ko Facebook. Idan wani ya saya ta link dinka, kai kuma za ka samu kashi 5% zuwa 30% na kudin. Misali, idan ka sayar da waya ta N100,000 za ka samu N10,000.
  3. Rubutu da Fassara (Freelancing)
    Idan ka iya rubutu da Hausa ko Turanci, akwai shafuka kamar Upwork, Fiverr, da kuma Seeking Alpha. Mutane suna biyan N5,000 zuwa N20,000 don a rubuta musu labari daya. Kana iya bude account a Fiverr ka rubuta “I will translate English to Hausa” – mutane da yawa daga kasashen waje suna bukatar haka.
  4. Koyar da Ilimi a Online (Selling Knowledge)
    Me ka iya? Girki? Dinki? Gyaran waya? Ilimin Crypto? Ka yi bidiyo ka koyar, sannan ka sayar a WhatsApp ko Telegram a kan N1,000 zuwa N5,000. Akwai wani bawan Allah a Kano da yake koyar da yadda ake hada turare a bidiyo, yana samun sama da N300,000 a wata.
  5. Blog da Google AdSense
    Kamar yadda muke yi a APA Hausa, ka bude blog. Ka rika rubuta labarai masu amfani kamar “yadda ake samun kudi” ko “girke-girke”. Idan mutane suka fara shigowa da yawa daga Google, ka nemi Google AdSense. Google zai rika saka talla a shafinka, kuma zai biya ka a duk dannawa.

Kammalawa

Samun kudi a internet ba karya bane, amma yana bukatar hakuri. Kada ka fada tarkon masu cewa “ka turo N2,000 ka samu N20,000”. Fara da hanya daya kacal, ka dage akai na watanni 3. Idan ka ga tana aiki, sannan ka kara wata.

Wanne daga cikin wadannan hanyoyin kake son mu yi maka cikakken bayani akai? Ka rubuta mana a comment.

Views: 57

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *