Sojoji sun bankaɗo gidan da ƴammata ke Haihuwar Jarirai suna siyarwa a Adamawa

Sojoji zun bankaɗo gidan da ƴammata ke Haihuwar Jarirai suna sayarwa a Adamawa

Rundunar sojin Najeriya ta bankado wani sansani da ake samar da jarirai ba bisa ka’ida ba a jihar Adamawa.

Rundunar ta bayyana kama wadanda ake zargi mutum bakwai tare da ‘yan mata 17 da ake tursasawa haihuwar jariran.


Wannan matsala ta zama ruwan dare a Najeriya musamman a Kudancin kasar da akafi samun yawaitar faruwar hakan
Jihar Adamawa – Rundunar sojin Najeriya ta kai samame sansanin haihuwar jarirai ba bisa ka’ida ba da safarar mutane a jihar Adamawa.

Yayin samamen, rundunar ta kama wadanda ake zargi mutane bakwai a maboyar da kuma ‘yan mata 17.

Sojoji Sun Bankado Sansanin Kyankyashe Jarirai Ba Bisa Ka’ida Ba A Adamawa
Wadanda Aka Kama A Sansanin.

Babban kwamandan yanki na 23, Birgediya Janar Muhammad Gambo shi ya bayyana haka ga ‘yan jaridu a Yola a yau Litinin 26 ga watan Yuni.

Kwamandan ya bayyana yadda suka samu sansanin tare da ‘yan mata da ake tursasawa.

Ya ce rundunar na aiki ne a bakin iyakar Najeriya da Kamaru lokacin da suka samu rahoton wannan sansani da ta’asar da ake yi, Daily Trust ta tattaro.

Ya kara da cewa sansanin na dauke da ‘yan mata masu shekaru tsakanin 19 zuwa 21 da suka kwashe fiye da shekaru 3 ba tare da sanin ‘yan uwansu ba.

Muhammad Gambo ya ce bankado wannan sansani ya kara tabbatar da karuwar safarar mutane da ake yawan samu a Najeriya, cewar Vanguard.

Ya yabawa sojojin yadda suka bankado sansanin haihuwar jariran
Ya yabawa rundunar sojin kan wannan nasara inda ya ce yana fatan wannan ya zama matakin farko na dakile wannan matsalar.

Ya ce:

“Wadanda ake zargin da kuma ‘yan matan da abin ya shafa an tafi da su zuwa hedkwatar rundunar da ke Yola.”

Views: 9

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *