Yadda Jami’an Ƴan sanda suka kama ma’aikatan jinya 2 bisa zargin sace Mabiyiya

Jami’an Ƴan sanda sun kama ma’aikatan jinya 2 bisa zargin sace Mabiyiya, sun ce Kare ya Cinye

Jami’an ‘yan sandan jihar Ondo sun kama wasu mutane uku da ake zargi da satar mabiyiya a asibiti bayan haihuwar jaririya.

Mutanen uku, wadanda suka hada da ma’aikatan jinya biyu da wani mai gadi guda daya an kama su ne a wata cibiyar lafiya da ke Owo a jihar
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami-Omisanya ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce mutanen uku na hannunsu.

Jihar Ondo – Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta cafke ma’aikatan jinya guda biyu da wani mai gadi bisa zargin sace mabiyiyar matar da ta haihu.

Wadanda ake zargin suna aiki ne a cibiyar lafiya ta Comprehensive a Emure Ile, Owo da ke cikin jihar Ondo.

‘Yan sanda sun kama ma’aikatan lafiya 2 da mai gadin asibiti bisa zargin satar mabiyiya a Ondo
Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Ondo, Funmilayo Odunlami-Omisanya.

Hoto: Peoples Gazette. Asali: Twitter

Daily Trust ta tattaro cewa an zarge su da sace mabiyiya bayan haihuwar jarirya bayan iyayen yarinyar sun kai rahoton zuwa ofishin ‘yan sanda.

Mahaifin jaririyar ya ce asibitin sun ki bai wa matarsa mabiyiyar
Mahaifin jaririyar, Tunde Ijanusi ya ce asibitin sun ki su bai wa matarsa mai suna Joy mabiyiya bayan ta haihu.

Ijanusi ya bayyana cewa duk kokarin da ya yi don samun mabiyiyar daga ma’aikatan asibitin ya ci tura.

Daya daga cikin kakannin jaririyar ta ce lokacin da ta samu likitocin akan mabiyiyar sai suka ce mata ai kare ne ya shiga asibitin ya cinye mabiyiyar.

Ta kara da cewa daga cikin ma’aikatan asibitin ya bukaci da su manta da abin don kada jama’a su san me ake ciki.

Yayin da tace ba su yi wata-wata ba suka kai rahoton ofishin ‘yan sanda don daukar mataki na gaggawa, cewar Tribune.

Rundunar ‘yan sandan jihar sun tabbatar da kama mutanen uku
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami-Omisanya ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce dukkan mutane ukun da ake zargi suna komarsu.

A cewarta:

“Muna kan binciken wadanda ake zargin su uku, kuma zamu binciko tushen abin don daukar mataki.”

Source: hausa.legit.ng

Views: 16

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *