Kamfanin Facebook sunyi Approving ƙasar mu Nigeria a cikin ƙasashen da zasu fara amfani da Facebook Stars domin masu Account a Facebook su fara samun kuɗi da Facebook..
Ƙasashen da kamfanin yayi Approving domin su fara amfani da Facebook Stars a Africa sune kamar haka:👇
- Egypt
- Kenya
- Madagascar
- Morocco
- Nigeria
- Sudan
A Post ɗina na ƙwanaki na faɗa maku akan cewa ko wace Star da mutun yasamu facebook zai biyashi dalar America $0.01 USD dai dai da 4.41 Naira, Musamman kuma idan ya kasance kai mutum ne mai yawan posting na Videos ko Reels to tabbas zaka iya dacen Facebook zai saka maka Facebook Stars ɗinka Automatically basai ka tura masu request na Applying ba, idan kuma ba’a saka maka ba to lallai dole sai kayi applying.
Akwai ƙa’idojin da ake cikewa kafin shiga tsarin dole ya kasance kanada followers a ƙalla guda dubu ɗaya (1k) sannan kuma cikin sauƙi zaka iya dubawa domin tabbatar wa kanka cewa shin ka cike ƙa’idojin da suke buƙata ko kuwa baka cike ba.
Hanyar da zaka iya ganewa shine idan kashiga cikin Profile naka ka danna wajen ɗigo-ɗigo guda ukun nan da suke a Profile ɗinka zai kai ka kai tsaye a Dashboard na Profile ɗin, daganan sai ka danna wurin da aka rubuta “Tools To Try” zakaga wurin da aka rubuta “Stars” sai ka danna shi anan ne zaka gani idan ka cika ƙa’idar.
Bayan ka cike ƙa’idojin da suke buƙata sai kuma kaje kayi Applying.
Abinda zakayi na farko shine zakaje wurin da aka rubuta “Tools To Try” sai ka sake danna wurin “Stars”, sannan sai kayi accepting “Terms And Condition” nasu tun daga nan zaka fara ganin Stars ɗin sun fara bayyana a post ɗinka, sai dai fa bazaka fara samun kuɗin dashi ba har sai ka seta da Payment Account dinka zasu tambayeka payment details dinka.
Sai kawai kayi amfani da “Bank account” naka ko “PayPal” sannan sai kayi uploading “Tax Form” naka, bayan kagama zasuyi Review na dukkan bayanan da katura masu domin tabbatar da gaskiyar bayanan idan naka ne.
Idan kanaso kaga stars ɗin da kasamu zaka iya shiga wurin da aka rubuta “Your Tools” anan wurin zakaga Stars ɗinka.
Note: Dole sai kana Professional Mode, kuma a yanzu ana Applying yin amfani da Stars din ne amma ba’a riga anyi Activating nata ba ko sun fara siyar da ita ba.
Allah yataimaka..
© Salisu Abdurrazak Saheel
Views: 17
