HANYAR MALLAKAR SAURAYI LOKACIN DAMUNA:
Budurwar wani abokina da zai kara aure da ita wallahi ita ta sama masa gonar shinkafa ta tilasta masa yin noma a wannan shekaran.
Da yake gonar a kusa da unguwarsu ne, kusan kullum sai taje tayi aiki a gonar.
Lokacin da ta fara kwadaita masa yin noman tace masa Yayana kaga kana da iyalai, ga yanayin rayuwa da ake ciki, inaga ka samu kayi noma zai taimaka wajen rage maka dawainiyar gida.
To yanzu haka gona tayi kyau, idan yaje hira da yamma sai ta jashi gona suyi ciro kuma suna dan hirarsu.
Yace haduwarsa da wannan yarinya wani arziki Allah ya nufe shi da shi.
Allah ya hada bayi da rabonsu na alheri ameen
source: sirrin riƙe miji da facebook
Views: 217
