Budurwa ta nemi saurayi ya bata Taliya yayi Zina da ita

TACE “KA BANI TALIYA KAYI ZINA DANI”

Daga shafin Aminu Harsanu Guyaba.

Yanzun nan nayi sallar Maghriba a ɗaya daga cikin Masallatan Jami’o’in da suke Jihar Bauchi, sai wani Malami ya tashi yayi nasiha yake cewa wani ɗan uwa ya same shi da wani kuka akan wani abu da ya faru da shi.

Yana zaune jiya da daddare sai wasu mata guda biyu suka zo wucewa a cikin Jami’ar sai ɗaya tayi gaba, ɗaya kuma ta dawo da baya zuwa inda yake, sai ta mishi magana akan cewa tana wani hali ne na rashin abinci, don Allah ya siya mata taliya guda ɗaya zata bashi dama yayi zina da ita.

Budar bakinsa yace mata shi ba haka yake ba, kuma bazai iya ba, sannan taji tsoron Allah, kuma bashi da taliyar da zai bata, amma dai ga ₦500 taje tayi wani abun da shi.

Wannan abune da yanzun nan Malam ya faɗa a Masallaci, adon haka shawari na ga Iyaye da kuma Yayu da suke da ƴan uwa a Makarantu shine suyi wa Allah suna kula da ƴaƴansu ko ƴan uwansu duk da dai munsan ana wani hali.

Amma fa Mata abin a lura dasu sosai ne, sanann ayi addu’a, wadanda suka kai na aure ayi musu musamman idan sun samu manemin da yake son su da gaske.

Allah ya tsaremu ya rufa mana asiri.

Views: 44

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *