Yadda wani Matashi ya shafe shekaru 29 yana neman Iyayen sa
Wani dan matashi dan Najeriya ya ce bai sake sanya iyayensa a idanunsa ba tun bayan rabuwarsu yana da wata biyar kacal a duniya.
Matashin mai shekaru 29 ya bayyana cewa har yanzu bai cire rai da cewa zai sake haduwa da iyayen nasa ba.
Ya ce mahaifinsa ma’aikacin Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Kasa (NEPA) ne da ke Ilorin kafin a kore shi, wanda hakan ya tilasta masa komawa Legas
Wani dan Najeriya, Adewole Idowu Oluwatobi, ya bayyana cewa har yanzu yana ci gaba da neman ‘yan uwansa da ya shafe shekaru 29 bai hadu da su ba.
A wani dogon sako na musamman da ya aikowa Legit.ng, matashin mai shekaru 29 ya ce ya rabu da iyayensa da ’yan uwansa uku sakamakon rabuwar da mahaifan nasa suka yi tun yana dan wata biyar a duniya.
Matashi ya shafe shekaru 29 yana neman iyayensa
Idowu ya ce har yanzu bai cire ran haduwa da iyayensa da ya shafe shekaru 29 yana nema ba. Hoto: Adewole Idowu Oluwatobi.
Ya ba da bayanan danginsa da ya rabu da su tun yana karami
Ya bayyana sunan mahaifinsa da Adefalu Adewole da ’yan uwansa Monday, wanda shi ne babba, da kuma Taiwo da Kehinde, wanda suka kasance tagwaye.
A cewar Idowu, mahaifiyarsa mai suna, Adeyemi Funke, ta fito daga Kabba da ke jihar Kogi, mahaifinsa kuma dan asalin Ilaro ne da ke jihar Ogun.
Ya kara da cewa iyayen nasa sun rayu ne a gidan mai lamba 23 dake titin zuwa Abeokuta a Alakija, daidai tashar motar Mushin Olosha da ke birnin Legas a shekarar 1987.
Ya kuma bayyana yadda mahaifinsa ya fara kasuwancinsa mai suna ‘Adesco Electrical Works’ a Legas bayan ya barin aikin na ma’aikatar NEPA da ya yi.
Tun da ya fara tasowa yake ta fatan haduwa da iyayensa
Matashin ya ce tun tasowar sa yake ta faman neman iyayen nasa da ‘yan uwansa, amma har yanzu dai ba wani bayani.
A cikin sakon da ya aikowa Legit.ng tare da hoton iyayen nasa, Idowu ya ce babban burinsa shi ne ya gan shi tare da iyayensa saboda shi ma ya ji yadda ake ji.
Ya kuma ce ba ya bukatar komai daga garesu illa kawai ya gansu a tare, sannan kuma ya yi fatan cewa mutane za su ci gaba da yada wannan sakon nasa har ya isa ga iyayen nasa.
Views: 16
