Bude dandalin batsa a WhatsApp, Facebook ya sa nayi wannan mafarkin—Safiyya

Wata baiwar Allah mai suna Safiyya ta bayyana yadda tayi wani mummunan mafarki mai cike da tsananin firgitarwa wanda duk mai imani idin yaji sai ya shiga tai tayinsa ga abinda ta ce.

“A daren jiya na kwanta bacci amma tunda baccin ya kwashe ni sai gaba daya hankali da ruhinna ya hasko min dandalin filin tashin Alkiyama, da farko dai nayi mafarkin an zare rai na wato na mutu, bayan an kaini kabari na an rufe ni sai aka tayar da ni aka dunga yi min azaba.

“Nau’i nau’in Azaba kuma aka ce min ba za’a bari ba har sai aikin sharrin da na gina a lokacin da ina rayuwata a duniya ya gushe sannan za’a daina yi min azabar, to ni dai a iya rayuwata da nayi a duniya na san cewa ban gina gidan Giya, Caca, gidan kallo da dai sauransu ba.

” Sai aka ce min ai na bude dandalin batsa a WhatsApp da Facebook, inda ake amfani da su wajen turo Hotuna da Bidiyoyi na batsa a cikinsu kuma ba za’a daina yi min azaba ba har sai an rufe wadannan dandalullukan, sai nace to a bani dama in koma duniya in dauki wayata in rufe sai a dawo da ni cikin kabari na, sai aka ce min ai idan an zo ba’a komawa.

“Sai na fashe da kuka aka dunga yi min azaba sai da aka dauki shekara guda ana min azaba babu dare babu rana, sai kwatsam naji an tsaya an daina yi min sai nace Allah ya gafartamin ne, sai aka ce a’a ai an rufe group dinne a yau shi yasa azabar ta tsaya, saboda na bawa wata kawata admin kuma lokacin da shiriya ta zo mata sai ta goge group din na WhatsApp da Facebook, shi yasa na samu saukin azabar.

” Ana cikin haka sai naji an kira Sallar Asubahi sai na farka a firgice naje nayi Sallah, bayan na dawo sai na bude data sai naga ashe ba’a goge groups din ba nan take na goge su sannan na share duk wani budiyo da hotunan batsa da suke cikin waya ta.

To kunji dai da fatan Allah ubangiji ya shirye mu shirin addinin musulunci ganin yadda wannan al’adar ta bude dandalullukan batsa ya zama kamar gasa a tsakanin matasan wannan zamani muna fatan Allah ya tsare mu masu yi kuma Allah ya shirye su.

Yan’uwa wannan mafarki da bawan Allah nan wa’azine saboda haka akwai bukatar a yada shi zuwa sauran groups don mu amfana Allah ya tsaremu ameen.

Views: 104

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *