NFF ta amince da sauya sunan gasar firimiya ta ƙasa

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF, ta amince da sauya sunan gasar kwallon kafa ta firimiya ta kasa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa ya bayar da rahoton cewa, an amince da sauya sunan ne a taron shekara-shekara na NFF karo na 79, AGA, a Uyo, jihar Akwa Ibom a jiya Lahadi.
A cewar sanarwar bayan taro da aka fitar, NFF ta amince da sauya sunan gasar mafi girma a ƙasar daga Nigeria Professional Football League, NPFL, zuwa Nigeria Premier Football League, NPL.
Ya ce amincewa da canza sunan na daya daga cikin kudurorin da aka yanke a taron.
Views: 64
