Wata sabuwa Namiji mai Gemu ya fiye min Miliyan 200

Abubuwan Da Aka Cimma A Tattaunawar ‘Yan Ƙwadago d5a Gwamnatin Najeriya
A ranar Lahadin da ta gabata ne gwamnatin Najeriya ta yi wani zama na musamman da shugabannin ƙungiyar ƙwadago na kasar NLC da TUC, kan matakan da za a ɗauka na magance taƙaddamar da ta biyo bayan cire tallafin man fetur da ake ta taƙaddama a kai.
Su dai ‘yan ƙwadagon sun shirya tafiya yajin aikin sai Baba-ta-gani a wannan makon yayin da ake tsaka da bikin cikar ƙasar shekara 63 da samun ‘yancin kai.
Sai dai yayin wani zama da shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya Femi Gbajabiamila, ya jagoranta tare da shugabannin ƙwadagon, an tattauna muhimman batutuwa don lalubo mafita.
Batutuwan da aka tattauna sun haɗar da amincewa da ƙarin albashin wucin gadi na Naira 25,000 ga ma’aikata, da kuma gaggauta samar da motoci masu amfani da gas don sauƙaƙa matsalolin sufuri, da cire tallafin man ya haifar.
Wani alƙawari kuma da gwamnatin ta yi shi ne na samar da Kuɗaɗe ga ƙananan masana’antu, da kuma cire harajin VAT daga iskar gas tsawon watanni shida, da rabawa gidaje miliyan 15 tallafin Naira dubu saba’in da biyar a wata uku, ma’ana Naira dubu ashirin da biyar a kowanne wata.
Matsayar Da Aka Cimma
Yayin taron na shugabannin ƙwadagon da kuma ɓangaren gwamnati dai an amince a kan cewa ba za a iya aiwatar da dukkan waɗannan manufofi ba, a yayin da ‘yan ƙwadago ke yajin aiki, don haka har sai sun fasa sun janye yajin aikin da suke so su tafi.
Kazalika shugabannin ƙwadagon sun buƙaci a sake duba ƙarin da aka yi a naira dubu ashirin da biyar, don haka wakilan gwamnati a zaman sun ce za su sake miƙa wa shugaba Tinubu buƙatar don ya yi nazari a kanta.
Gwamnatin Tarayya za ta fara biyan N75,000 ga gidaje miliyan 15 akan naira 25,000 duk wata, na tsawon watanni uku daga Oktoba zuwa Disamba 2023.
An cimma matsaya a kan cewa za a kafa wani ƙaramin kwamiti da zai tabbatar da aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma, kana ƙungiyoyin na NLC da TUC za su yi nazari a kan tayin da Gwamnatin Tarayyar ta yi, da manufar fasa tafiya yajin aiki.
Sauran waɗanda suka wakilci gwamnatin Najeriya a zaman sun hadar da Ministan Kuɗi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun, da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da kan jama’a Mohammed Idris, da Ministan Ƙwadago Simon Lalong, da Ƙaramin Ministan Ƙwadago, Nkeiruka Onyejeocha, da Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare Tattalin Arziki, Abubakar Atiku Bagudu, Ministar Agaji da Yaƙi da fatara Betta Edu, da Ministan ciniki da Masana’antu da Zuba Jari, Doris Uzoka-Anite, da Shugaban Ma’aikata na Tarayya, Dr. Folasade Yemi- Esan da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu.
Views: 23
