Kwankwasiyya a jinina take Nana Yola

Da dawowa ta Kano ke da wuya ranar Juma’ar da ta gabata na nufi babban asibitin Sir Sanusi, ɗaya daga cikin tsofaffin manyan cibiyoyin kiwon lafiya na jiharmu ta Kano.
A lokacin ziyarar, wanda wani bangare ce na al’adata domin na ganewa ido na irin abubuwan dake wakana a ma’aikatu, naji ba daɗi matukar gaske yadda na ga yadda asibitin ke cikin mawuyacin hali saboda rashin kulawar gwamnatin baya.
A yanzu haka tuni na riga na bayar da umarnin gudanar da aikin gyaran gaggawa na asibitin domin tabbatar da cewa marasa lafiya da ma’aikatan lafiya suna rayuwa a ƙarƙashin yanayin da ya dace.
Haka kuma yayin wannan ziyarar, na samu wata ma’aikaciyar lafiya mai suna Khadija Adam, wadda take tallafa wa marasa lafiya tare da aiki tuƙuru duk da rashin kyawun yanayi na wannan asibiti saboda haka na bayar da umarnin a ɗauke ta aiki nan take a matsayin ma’aikaciyar dindindin.
Haka kuma dukkan majinyatan da ke kwance a asibitin sun samu kudi Naira Dubu Ashirin kowanne, a matsayin agajin gaggawa. – AKY
Views: 83
