
An shawarci ma’aikatar kula da harakokin wajen tarayyar Najeriya, wato Ministry Of Foreign Affairs, da ta nemi gwamnatin kasar Burtaniya ta taso keyar shahararren dan tada kayar bayar nan na yankin Naija Delta, wato Nnamdi Kanu, zuwa Najeriya domin ya fuskanci hukunci.
Wani gun gun gamayyar kungiyoyin yan Najeriya mazauna kasashen ketare ne suka nemi ma’aikatar da ta sa a dawo mata da Nnamdi Kanun zuwa Najeriya, saboda irin kalaman tayar da zaune tsayen da yake yi a wajen kasar tare da tunzura magoya bayansa.
Domin su tayar da hargitsi a kasar dai dai lokacin da kasar ke fama da tarin matsalolin da suka addabe ta musamman matsalar tsaron da ta yi tsamari a kusan daukacin yankunan kudanci da arewacin kasar.
Menene ra’ayoyinku shin kuna ganin ya kamata a dawo da shi gida?
Views: 37

Allah yasa akannan yafi alheri,