VIDEO: “Najeriya ba zata wuce nan da 2024 ba zata wargaje mun gama shiri”—Amurka

Ku latsa nan don kallon Bidiyon

Tsohon jakadan kasar Amurka a tarayyar Najeriya John Cambel, ya bayyana cewa Najeriya ta gaza ta ko wane fanni na jinkan yan kasarta sannan bata da madogara kuma bata da wata makoma mai kyau nan gaba, saboda haka abune mawuyaci ta wuce shekarar 2023 bata wargaje ba in ji shi, kamar yadda ya bayyana a wata mujallar da ake wallafawa a kasar Amurka.

Sai dai a nata bangare gwamnatin kasar ta bakin mai magana da yawun fadar shugaban kasa, ta mayar da martani kan wadannan munanan kalaman da John Cambel, ke yi a kan kasar inda ta ce, “Idan Yan Najeriya zasu tuna wannan mutumin John Cambel ya yi hasashen wargajewar Najeriya, a zaben 2015 amma Allah ya tsallakar da kasar burinsa bai cika ba.

Babu wani abu na alheri da yake fatan samun Najeriya sai sharri da karya, kuma kasar da aka ce bata da iko da iyakokinta da jakadancin kasashen duniya, ita ce za ace ta kamo hanyar wargajewa ba Najeriya ba” in ji mai magana da yawun shugaban kasa.

Kunji fa menene ra’ayoyinku kan wannan batu, mu dai muna fatan Allah ya ci gaba da tsare Najeriya daga sharrin masu sharri sannan ya kawo mana dawwamammen zaman lafiya a fadin kasar nan ameen

Views: 26

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *