Gwamna, matawallen jihar Zamfara ya sanar da ranar da zai koma APC

Gwamna Matawallen Jahar Zamfara  zai canza sheka daga jam’iyyar People Democratic Party PDP zuwa jam’iyyar All Progressive Congress APC a ranar  12 ga watan June, 2021. kamar yadda  Jaridar Premium Times ta ruwaito tun gabanin wannan sanarwa dai a ranar yau gwamnan ya rusa majalissar zartaswar jihar.

Rusa Majalisar zartaswa ta jahar Zamfara da Gwamna Bello Muhammad Mutawallen Maradun yayi yana daya da ga cikin shirye-shiryen sa na sauya sheka da ga Jam’iyar sa ta PDP zuwa Jam’iyar Adawa ta APC mai mulkin Najeriya.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa wani makusanci gwamna Mutawallen Maradun ne ya tsegunta musu wannan labari na Shirin ficewar sa daga jam’iyyar a ranar jun 12, dama dai tun a farkon wannan makon da muke cike ne aka soma yada rahotannin ficewar gwamnan na jihar ta Zamfara daga jam’iyyarsa ta PDP.

Ko a makon daya gabata ma saida gwamnan jihar Abia da ke kudancin kasar ya fice daga jam’iyyar PDP ta adawa zuwa APC mai mulkin kasar.

Kunji fa menene ra’ayoyinku?

 

Views: 50

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *