Abida nayi bayan abokai sun kai ni ɗakin amarya

Ba a son bayar da labarin abin da ke gudana tsakanin Ango da Amarya. Yin hakan ya sabawa karamci da mutunci. A bisa al’adar samarin Hausawa, in mutum ya yi sabon aure, abokinsa kan kusance shi a tsawon kwanakin amarci don shan labari na yadda abubuwa ke gudana tsakanin sa da amarya. Ya kamata ma’abocin hankali ya guji tozarta mutuncin iyalinsa, don in ka bai wa abokinka labarin sirrin da ke gudana tsakanin ka da amaryarka, duk lokacin da suka gan ta za su riqa ganin abin ne a fuskarta. Hakan kuwa tozarci ne gare ta.

Musulunci ya hana musulmi fadin sirrin kwanciya da nau’in wasannin sha’awa da ke gudana tsakanin sa da matarsa. Yin hakan laifi ne. Abu Sa’eed ya ruwaito hadisi daga Manzon Allah (S) ya ce, Mafi sharrin mutane matsayi a wurin Allah ranar alkiyama shi ne mutumin da ke kunyata matarsa (ta hanyar ba da labarin sirrin kwanciyar da ke gudana a tsakanin su) da kuma (mace) mai kunyata mijinta “(Musnad Ahmad).
Wani sahabin Manzon Allah (S) ya ce, “Wata rana mun yi salla da Manzon Allah (S). Bayan ya sallame, sai ya fuskanto mu ya ce, “… Shin a cikinku akwai wanda in ya sadu da iyalinsa yakan rufe qofa ya lullubu da mayafi, Sa’annan kuma ya fito waje yana ba da labari, ya ce, Na yi abu kaza da kaza da iyalina? Sai muka yi shiru. Sai ya juya ga (taron) mata ya ce, Shin a cikinku akwai mai bayar da (irin) wannan labari? Sai ‘yar gidan Ka’abu ta tashi durkushe a kan gwiwowinta don Manzon Allah (S) ya gan ta kuma ya ji zancenta, ta ce “Eh, na rantse da Allah (ya Manzon Allah!) maza suna bayar da (irin wannan) labarin, kuma mata ma suna bayarwa! “Sai Manzon Allah (S) ya ce “Shin kun san misalin wanda ya aikata haka? Misalin wanda ya aikata haka, kamar Shaidan ne da Shaidaniya suka sadu da junansu, ya biya bukatarsa da ita (matar tasa) mutune suna kallon su. ” (Abu-Dawud, 130).

A zahiri, wannan hadisi ya nuna mana illa da munin bayar da labarin sirri na ma’aurata, in ba da wata Lalura ba.

Shamsuddeen M Sani.

Views: 143

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *