
ALLAHU AKBAR:
Rayuwar Sadiya Aliyu Wamkko Abi Koyi Ce;
Sadiya Aliyu Wamakko ‘ya ce ga tsohon gwamnan jahar sokoto Dr Aliyu Magatakarda Wamakko,wacce duk wata dama da dan adam yake nema na gatanci a duniya Sadiya ta sami wannan dama.
Amman cikin ikon Allah Sadiya ta kasance tayi fatali da wannan jin dadi na rayuwar duniya, ta rungumi bautar Allah da neman tsira a ranar gobe Qiyama. A maimakon irin yanda wasu ya’yan masu kudi da mulki su ke gudanarda rayuwarsu ta hanyar shagaltuwa da duniya.
Sadiya tun tana karama har zuwa girmanta ba ka isa ka raba da Hijabi ba, sannan duk abinda take yi matukar akace lokacin sallah yayi zata bar shi har sai tayi sallah. Sannan duk sanda ta samu dan lokaci za ka ganta tana karatun alqur’ani mai girma ne.
Wani lokaci Qawayen Sadiya har tsokanarta su ke yi cewa bata waye ba, saboda kasancewar duk inda ka ganta za ka same ta cikin shiga irin wadda addinin msulunci yace a yi ne, kamar ba diyar wani babban mutun ba, irin yanda wasu ya’yan masu kudi ‘yan zamani ke yi.
Sannan Sadiya ta kasance matukar ta maka wani abu wanda ba dai-dai ba nan take zata baka hakuri, matukar ta lura cewa ranka ya 6aci. Wani lokacimma haka kawai Sadiya take neman gafara ga yan uwan ta, koda kuwa bata misu komai ba. Domin kasancewar ta yarinya mai matukar hankali da biyayya da kuma tsananin son jama’a.
Bayan ta kammala Secondary Sadiya batayi wata-wata ba nan take ta fidda mijin aure don raya sunnar manzo. A maimakon cigaban da karatun boko kamar yanda wasu ya’yan masu kudi ke yi, ta hanyar zuwa kasashen turai a kwashe shekaru da shekaru da sunan neman ilimin boko.
Sai dai a bangaren Sadiya bata yarda da wannan ba, sai ta zabi yin auren don raya sunnar manzo, dudda kasancewar tanada damar zuwa duk wata kasa da take son zuwa a duniyar nan, saboda a lokacin mahaifin ta gwamnan ne. Amman sai ta zabi yin aure saboda ilimin addini da Allah ya kaddare ta da samu da kuma yin aiki da shi.
Irin riko da addini da Allah ya baiwa Sadiya, ‘yar da ta haifa tun tanada shekara 3 a duniya ta fara koyarda ita karatun alqur’ani mai girma da kuma yin sallah. Kuma yanzu haka wannan yarinya tanada shekara 5 a duniya, ta iya sallah da karatun alqur’ani kamar yanda mahaifiyar ta Sadiya ta nuna mata.
Amman da yake rayuwa ba tabbas an wayi gari Allah ya karbi ran Sadiya a wajen haihuwa, yau shekara daya.
Ya Allah ka jikan wannan baiwa taka da rahama.
S-bin Abdallah Sokoto
Views: 30
