Tsohon gwamnan jihar Kano Eng Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana irin ƙudurorin da yake fatan aiwatar wa a duk lokacin da ya samu damar ɗarewa kan kujerar shugabancin Najeriya.
Sanata Kwankwaso ya bayyana cewar abin takaicin da ya fi damun sa a ƙasar nan shine yadda aka mayar da harakar ilimi koma baya, wannan yana ɗaya daga cikin abubuwan da suke ci masa tuwo a ƙwarya, inda ya ce.
Hatta matsalar tsaro da talaucin da su ka addabi ƙasar nan ba komai ya jawo su ba face rashin baiwa ƴaƴan talakawa cikakke kuma ingantaccen ilimi inda ya ce shi fa idan Allah ya ba shi damar zama shugaban Najeriya babu shakka waɗannan abubuwan guda 8 sune zai maida hankali a kansu.
1-Ilimi
2-Tsaro
3-Kiwon Lafiya
4-Noma
5-Samar Da Ayyukan Yi Ga Matasa
6-Gyara Masana’antu
7-Gina Sabbin Masana’antu
8-Jawo Masu Zuba Jari Daga Ƙasashen Duniya
Waɗannan in sha Allahu idan Allah ya ara mana dama muka karbi mulki sune abubuwan danza mu fi mayar da hankali a kansu.
Views: 11
