Abubuwa biyu da ke sa gashin macce yayi yawa da tsawo kamar na ƴaƴan Turawa

Assalamu alaikum tare da fatan ana lafiya. Gyaran jiki musamman ga mace na da muhimmanci sosai. Domin mata da dama wadanda suke da kananan shekaru idan jikinsu ba ya samun sinadaran da suka kamata akwai matsala. Sai a ga fatar jiki tana yankwanewa. Yankwanewar fatar na sanya mace tsufa da wuri.

Don haka, dole ne a rika kula da fatar jiki da gashi da sauran gabobi.

  • Gashi; a samu ayaba da kwai a cire kwaiduwar sannan a kwaba tare da ayaba sai a tsaga gashi a shafa a fatar kai hade da gashin kai sosai. A bari na tsawon minti goma zuwa ashirin sannan a wanke da man wanke gashi. Yin haka na sanya karfin gashi kuma yana hana shi zubewa sannan yana sanya shi sheki.
  • Farce; a samu zuma a rika shafawa a farce na tsawon minti biyar akalla sau daya a mako domin sanya farce laushi da sheki sannan za a iya shafa zumar a fuskar domin magance kurajen fuska.

Views: 28

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *