Mutuwa wata aba ce mai matukar firgitarwa da tsoratarwa amma akwai wasu daga cikin bayin Allah makusantan sa masu matukar tsohon sa yana sassauta musu a yayi da suka zo mutuwa.

Shaikh muhyideen Al kurdi na daya daga cikin sanannun malaman da ke koyar da karatun Kur’ani tun yana Dan shekaru 25 har zuwa shekaru 97 da Allah Ya karɓi rayuwarsu.
Ya taba cewa, shi ya godewa Allah da bai yi suna a kan komai ba sai karantar da Kur’ani
Lallai Sheikh ya shiga kabarinsa yana Murmushi.
Muna fatan Allah Ya jaddada wannan rahama a gare shi tare da dukkanin sauran bayin Allah waɗanda suka riga mu gidan gaskiya.
A wani labarin kuma.
Ƙasar Saudiyya ta raba naman hadayar Hajji ga mutane miliyan 30 a kasashe 27 na Duniya
Saudiyya na Amfani da Dabbobin Layya, wanda kuma aka fi sani da Adahi, ko Hadaya, kwanan nan ya raba naman hadaya ɗin mai yawa ga kasashe da dama.
Rabon da aka yi ya haɗa da dabbobin hadaya guda 3,000 da aka aika kowacce zuwa kasashen Azerbaijan, Mali, Mozambique, Chadi da Gambia, 4,000 zuwa Nijar da 5,000 zuwa Djibouti.
Ƙasashen da aka gudanar da aikin rabon naman dai mafi akasarin su ƙasashe ne matalauta ko kuma marassa ƙarfi inda ko wace daga cikin Waɗannan ƙasashen suka amfana da nasu kason.
Wannan shiri dai na zuwa ne a matsayin tsawaita ayyukan agajin da jin-ƙai da masarautar kasar ke aiwatarwa a kasashe da dama karkashin umarnin Sarki Salman da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman.
Tsarin rarrabawar ya ƙunshi ƙungiyoyi da daban-daban na jin-ƙai, ƙarƙashin kulawa da bin diddigin kwamitin da gwamnatocin da su ka amfana su ka kafa.
Wakilan aikin daga kungiyar Bankin Raya Musulunci ta Duniya da jami’an haɗin gwiwa daga gwamnatocin kasashen su ma sun halarci aikin rabon wanda aka gudanar.
Views: 10
