Tsoho ɗan shekara 80 ya kasa samarin wata budurwa ƴar shekara 17 a Bauchi inda ya aure ta

Hausawa na cewa Soyayya ruwan zuma wani lokacin kuma ruwan maɗaci a nan dai wani dattijo ne ya angwance da amaryarsa a jihar Bauchi.

Dattijon ɗan kimanin shekaru 80 ya angwance ne da amaryarsa mai shekaru 17 da haihuwa bayan ya kasa samari a dare ɗaya kamar yadda shafin Rariya ya wallafa hotunan sa muna fatan ya sa alheri ya basu zaman lafiya.

A wani labarin kuma

Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasar nan ASUU tace gwamnatin Soja Ta Fi Ta Farar Hula Tausayin Malaman Jami’a

Shugaban Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce gwamnatocin mulkin soja na baya a Najeriya sun fi ta farar hula mai ci a yanzu tausayinsu.

Ya bayyana haka ne ranar Alhamis a Abuja, yayin kaddamar da wasu littattafan manyan makarantu guda 50 da wasu marubuta suka wallafa.

Hukumar da ke Kula da Manyan Makarantu ta Najeriya TETFund ce dai ta dauki nauyin wallafa littatafan.

A cewar Shugaban, “A shekarar 1992, lokacin da muka yi yajin aiki, sai muka bukaci a kalubalance mu, mu kawo mafita kan yadda za a samo kudaden da za a aiwatar da yarjejeniyoyin da aka amince da su.

“Haka aka yi kuwa suka kalubalanci ASUU, inda ko kwana uku ba a yi ba muka kawo batun kafa TETFund, wacce kuma gwamantin mulkin soja ta wancan lokacin ta amince. Ni ina ga gwamnatin soja ta ma fi ta farar hula tausayinmu.

“Yadda aka yi aka sami hukumar TETFund ke nan. An rattaba hannu a kan kudurin ya zama doka a 1993. Sai da ASUU ta sake komawa yajin aiki a karo na uku kafin a fara fitar wa TETFund kudi,” inji Shugaban ƙungiyar na ASUU.

Dangane da matakin “babu aiki babu albashi” na Gwamnatin Tarayya da ya kai ga malaman suka shafe wata takwas suna yajin aiki a bara kuwa, Farfesa Emmanuel Osodeke ya roki ’yan Najeriya da su dada matsa wa gwamnati lamba ta ceto manyan makarantun kasar daga durkushewar da suke barazanar yi.

Shi ma da yake jawabi yayin kaddamar da littattafan guda 50, Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ya ce sabbin littattafan za su rage kaka-gidan da na ketare ke yi a manyan makarantun kasar.

Adamu, wanda Minista a Ma’aikatar Ilimi, Goodluck Nanah Opiah ya wakilta, ya ce an yi lokacin da kusan dukkan makarantun Najeriya suka ta’allaka da na ketare, duk kuwa da makudan kudaden da ake kashewa wajen musayar kudade kafin sayo littattafan karatun ɗalibai.

Views: 20

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *